Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kongo za ta kara da Guinea a matakin kusa da dab da na karshe na gasar AFCON din 2023./ Hoto: AFP

Golan Masar Mohamed Abou Gabal ya barar da fenareti a bugun daga kia sai mai tsaron gida a wasan da Jamhuriyar Dimokuradiyar Kongo ta yi nasara da ci 8-7 bayan sun yi canjaras 1-1 a karawar matakin sili-daya-kwale na AFCON da suka yi ranar Lahadi a San Pedro .

Fenaretin da Abou Gabal ya buga ya daki 'fol' yayin da Lionel Mpasi ya zura fenareti a ragarsa lamarin da ya fitar da kasar da ta ci gasar AFCON sau bakwai daga gasar ta bana a filin wasan Laurent Pokou, inda 'yan Kongo suka barke da murna.

Ranar Juma'a ne dai Kongo za ta kara da Guinea a Abidjan.

Meschack Elia ya zura wa Kongo kwallo a ragar Masar a lokacin da ya ci kwallo da kai, sai dai kuma bai wuce minti tara ba Masar ta farke kwallon ta hannun Mostafa Mohamed wanda ya zura kwallo a ragar Kongo ta bugun fenareti .

An bai wa dan wasan tsakiyar Masar Mohamed Hamdy jan kati a karin lokaci inda 'yan wasan Pharaohs, wandanda gwarzonsu Mohamed Salah yale jinya, suka daina kai samame, kuma suka tsare gida har wasan ya kai ga matakin bugun fenareti.

Rashin iya karkare wasa a lokaci

Shekara 50 da ya wuce ne dai Kongo ta doke Masar a gasar cin kofin Afirka a matakin dab da na karshe kuma Kongo ta samu ta lashe kofin na wancan shekarar.

Wasan ya kasance canjaras na hudu da kasashen suka yi a jere a Côte d'Ivoire a wannan shekarar, ko da yake wannan ne canjaras na shida a jere da Masar ta yi tun gasar cin Kofin Afirkan da aka yi a Kamaru, kuma lokaci na biyar a jere da Masar take kai wa matakin karin lokaci a zagayen sili-daya-kwale.

Rashin zura kwallon da za ta raba gardama ya sake damun Masar don ba su iya karkare wasan cikin minti 90 ba.

TRT Afrika