An rage hukuncin haramcin buga ƙwallo da aka yi wa Paul Pogba, daga shekara huɗu zuwa watanni 18. / Hoto: AFP

Bayan samun ragin hukuncin haramci na shekaru huɗu daga buga ƙwallo, zuwa watanni 18, sakamakon laifin shan ƙwayoyin ƙara kuzari, ɗan wasa ɗan asalin Faransa, Paul Pogba yana burin dawowa filin wasa.

Pogba na fatan komawa taka leda a watan Maris mai zuwa, duk da ana tababar ko zai ci gaba da wasa a Juventus ta Italiya, kuma ana raɗe-raɗin zai koma Marseille ta Faransa a kakar cinikin 'yan wasa ta Janairun baɗi.

Kwantiragin da Pogba yake da ita da Juventus ba za ta ƙare ba sai bazarar 2026, amma an ruwaito ƙungiyar tana ƙoƙarin nemo hanyar rabuwa da shi da zarar ta samu dama.

Shafin Goal.com ya ambato jaridar Gazzetta dello Sport tana ce Pogba ya amsa cewa ƙaunarsa ga Juventus tana nan daram, kuma ya shiya saryar da kuɗi don komawa taka leda.

Na ƙagu na dawo

Pogba ya ce, “Ina shirye na haƙura da kuɗi don na sake buga wa Juventus wa. Ina so na dawo buga ƙwallo”.

Sadaukarwar Pogba don ya nuna cewa da sauransa a ƙungiyar tana nan, kuma ya jaddada cewa ƙwazonsa ne zai gaskata hakan, ba kalamansa ba.

Sai dai duk da zumuɗin Pogba na ya koma wasa, kocin Juventus, Thiago Motta bai nuna karsashi kan batun ba, inda ya ce ƙungiyar za ta "yi nazari" kan batun na Pogba saboda "ya yi tsawon lokaci bai buga ƙwallo ba".

Tun bayan zuwansa birnin Turin a 2022, Pogba ya buga wa Juventus wasa ne sau tara kacal. Hakan da kuma batun shari'arsa ya janyo zargin ƙungiyar na tunanin sallamarsa nan kusa.

Baya ga wannan, akwai batun cewa lambar rigar da Pogba yake sakawa, wato lamba 10 an bai wa Kenan Yildiz, ɗan asalin Turkiyya tun a kakar da ta gabata.

A yanzu dai a gasar Seria A, ba a ci Juventus wasa ba, kuma wasanta na gaba zai kasance da Lazio a wannan Asabar ɗin.

Ƙungiyar na mataki na uku a teburin Serie A da maki 13 daga wasannin 7, inda Napoli da ke kangaba, take gabanta da maki 3.

TRT Afrika