Wakilin dan wasan kwallon kafa dan asalin Nijeriya, Victor Osimhen, wanda ke taka leda a kulob din Napoli a gasar Serie A ta Italiya, ya fada cewa, ‘Da mun so barin Napoli, da mun ce za mu bari’.
Roberto Calenda wanda ke wakiltar dan kwallon, ya ce shi da dan wasan sun yi farin cikin ci gaba da kasancewa a kungiyar ta Napoli, bayan sanar da cewa dan wasan ya tsawaita kwantiraginsa da kulob din da ke rike da kofin Serie A.
A ranar Asabar ne gwarzon dan wasan kwallo dan asalin Nijeriya, Osimhen ya sanya hannu kan sabuwar kwantiragi da Napoli har zuwa bazarar 2026.
Sanya hannun da dan wasan ya yi ya kawo karshen rade-radin cewa yana shirin barin kulob din a bazarar badi, lokacin cinikin 'yan wasa.
A kwantiragin da Osimhen ya rattaba wa hannu, akwai sadarar barin Napoli, amma zuwa kulob din da ke wajen Italiyam kadai. Ana hasashen an saka wa Osimhen farashin Euro miliyan 120 zuwa 130, kuma ana ganin ba zai wa manyan kungoyoyin Turai tsada ba.
A hirar da Roberto Calenda ya yi da jaridar Corriere dello Sport, ya ayyana sabuwar kwantiragin ta Osimhen a matsayin mai "matukar tarihi".
A kakar bana, duk da cewa Osimhen ya yi fama da jinya, ya yi nasarar cin kwallaye 7. Kuma shi ne ya jagoranci Napoli har suka ci gasar Serie A ta bara, bayan sun yi shekara 33 rabonsu da cin gasar.
Haka kuma, Calenda ya ce, “A bazarar bara, an samu tayi da dama masu makudan kudi daga masu son siyan Osimhen daga gun Napoli. Da mun so mu tafi, da mun ce za mu tafi".