Hukumar ƙwallon ƙafar Kamaru ta ce ta yi mamakin jin cewa ma'aikatar wasanni ta ƙasar ta sanar da naɗa sabon koci na tawagar maza ta ƙasar, mai suna Marc Brys.
Ranar Laraba ne Hukumar ta soki yadda ma'aikatar wasanni ta ƙasar ta yanke shawarar ɗaukar sabon kocin "a karan-kanta".
Ma'aikatar wasannin ta hayo ɗan ƙasar Belgium, Marc Brys mai shekaru 61 a duniya don ya maye gurbin Rigobert Song, wanda ba a sabunta kwantiraginsa ba, bayan da aka fitar da ƙasar daga gasar kofin ƙasashen Afirka a matakin 'yan-16.
A wata sanarwa da ta buga a Fabebook, hukumar ta ce, "Hukumar ƙwallon ƙafa ta samu labarin, daidai lokacin da duka 'yan Kamaru suka samu labari, naɗin muƙami a tawagar ƙwallon ƙafar maza ta ƙasarmu".
Hukumar da aka fi sani da Feca foot, ta bayyana "matuƙar mamaki" kan abin da ya faru, wanda ta ce ya saɓa wa dokar ƙasa da ta shafi harkar ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa na ƙasa.
'Abin takaici'
Fecafoot ta ƙara da cewa tana ƙoƙarin "fito da batun abin takaicin fili", amma ba ta ba da cikakken bayani ba, bayan da kamfanin dillancin labarai na AFP ya tuntuɓe su.
Hukumar ƙwallo ta duniya FIFA, ba ta amincewa gwamnati ta tsoma baki a harkar gudanar da wasanni na ƙasa ba.
Sabon kocin, Brys shi ne koci na uku ɗan Belgium da zai riƙe ƙungiyar ta Kamaru. Na ƙarshe shi ne Hugo Broos, wanda ya jagoranci ƙasar ta ci kofin AFCON a karo na biyar a shekarar 2017.