Rahotanni sun ce Rashford bai ji ciwo a hatsarin da ya yi ba. Hoto/Getty Images

Dan wasan gaban Ingila da Manchester United Marcus Rashford ya yi hatsari a hanyarsa ta komawa gida bayan kungiyarsa ta Manchester United ta yi nasara kan Burnley a ranar Asabar.

Bidiyon da ake yadawa a shafukan sada zumunta ya nuna motarsa fara kirar Rolls Royce a gefen titi bayan ta yi hatsarin.

Jaridun Ingila sun ruwaito cewa dan wasan bai ji rauni ba a hatsarin da ya rutsa da shi.

Rashford ya buga wasa na mintuna casa’in a filin wasa na Turf Moor inda kungiyarsa ta Manchester United ta ci Burnley 1-0, kwallon da Bruno Fernandes ya ci.

Wannan ne karo na farko da Manchester United ke cin wasa bayan kungiyar ta yi rashin nasara a wasanni uku da ta yi a jere.

TRT Afrika da abokan hulda