Aliou Cissé yana shirye-shiryen gudanar da taron manema labarai ranar Juma'a domin sanar da shirinsa na jagorantar wasannin neman cancantar shiga gasar Afcon ta 2025 lokacin kafin a sanar da korarsa daga aiki.  / Hoto: AFP

An kori kocin Senegal Aliou Cissé daga aiki ranar Laraba, wanda ya jagoranci tawagar ƙwallon ƙafar ƙasar wajen lashe gasar Afcon da halartar gasar cin Kofun Duniya sau biyu.

Hukumar kula da tawagar ƙwallon ƙafar ƙasar ta bayyana cewa gwamnati ce ta hana ta sabunta kwantaragin Cissé.

Cissé ya kwashe kusan shekaru 10 yana jagorantar tawagar Teranga Lions wadda sau biyu tana zuwa zagayen ƙarshe na gasar AFCON — inda ta lashe gasar sau ɗaya a shekarar 2022 — tare da zuwa zagayen 'yan 16 a Gasar Kofun Duniya ta 2022. Senegal ta halarci gasar wadda aka gudanar a Qatar ba tare da fitaccen ɗan wasanta Sadio Mané ba, wanda ya ji rauni.

Hukumar ƙwallon ƙafar Senegal ta fitar da wasiƙa ranar Laraba inda ta gode wa Cissé bisa aikin da ya yi tare da “kyakkyawan sakamako. ”

Tsohon ɗan wasan na Paris Saint-Germain yana shirin gudanar da taron manema labarai ranar Juma'a domin sanar da shirinsa na jagorantar wasannin neman cancantar shiga gasar Afcon ta 2025 lokacin kafin a sanar da korarsa.

Kazalika wasiƙar ta bayyana dalilan da suka sa ma'aikatar wasanni ta ƙi sabunta kwantaragin Cissé da ƙarin shekara daya da suka haɗa da: gaza cika sharuɗɗan shiga gasa da gazawar tawagar wajen cika ƙa'idojojin FIFA, da kuma yiwuwar samun saɓani tsakanin tawagar ƙwallon ƙafar ƙasar da 'yan ƙasar ta Senegal.

TRT Afrika