Kungiyar kwallon kafa ta kasar Guinea Syli National, ta lallasa Nijeriya da ci 2 da nema a wasan zumunta da suka buga a babban birnin Hadaddiyar Jamhuriyar Larabawa, Abu Dhabi.
A tsakar ranar Litinin ne aka buga wasan a filin wasa na Bani Yas Stadium, gabannin tawagogin kasashen biyu su yi balaguro zuwa kasar Ivory Coast inda za a fara gasar cin kofin kwallon kafa ta Afirka, wato AFCON.
Jose Peseiro ne ke jagorancin tawagar Nijeriya, amma bai saka gwarzon kwallon kafar Afrika na wannan shekara ba, wato Victor Osimhen. Shi kansa kyaftin din tawagar, Ahmed Musa sai a minti 83 aka sako shi.
A minti 20 na wasan dan wasan Nijeriya na gaba, Simon Moses ya barar da bugun durme da ya samu, wanda ya janyo aka tafi hutun rabin lokaci Guinea tana da 1 Nijeriya tana nema.
Bayan awa daya da minti hudu da fara wasan, sai Guinea ta zura kwallo ta biyu, wanda daga shi ne ba a sake zura kwallo ba, har aka tashi suna da ci biyu, Nijeriya ba ta da kwallo daya.
Kasancewar wannan wasan na zumunta da kasashen biyu suka buga, shi ne na karshe kafin a bude gasar AFCON, ranar Asabar 13 ga watan Janairu. AFCON 2023 shi ne karo na 34 na gasar.
Za a iya cewa tawagar kasar Guinea ta samu karfin gwiwar fara buga wasanta a ranar farko da bude gasar AFCON 2023, inda za ta kara da mai masaukin baki, Kwadibuwa.
Nijeriya kuwa za ta buga wasanta na farko ne ranar Lahadi, kwana daya bayan bude gasar, inda za ta kara da Equatorial Guinea, a filin wasa na Stade Olympique Alassane Ouattara, da ke birnin Abidjan.