Otto Addo koci ne mai aikin neman 'yan wasa a Borussia Dortmund. / Hoto: Getty Images

Otto Addo ya dawo a karo na biyu, a matsayin kocin tawagar maza ta ƙasar Ghana, bayan da ƙungiyar Borussia Dortmund ta Jamus ta amince ta sake shi daga aikinsa na nemo mata 'yan wasa, a ƙarshen kakar bana.

Addo ya taɓa horar da tawagar Ghana na wucin gadi a shekarar 2022, har lokacin gasar Kofin Duniya da aka yi a Qatar, lokacin da Ghana ta doke Koriya ta Arewa amma daga baya aka fitar da ita a matakin rukuni.

Zai dawo aikin ne kan kwantiragin watanni 34, tare da zaɓin tsawaita wa'adin da ƙarin shekaru biyu, kamar yadda Ƙungiyar Ƙwallon Ƙafa ta Ghana ta ambata a Facebook.

Kwantiragin za ta ɗauki aƙalla har zuwa lokacin gasar Kofin Ƙasashen Afirka ta 2025, da kuma gasar Kofin Duniya ta 2026.

Simeon-Okraku ya faɗa a Instagram cewa Ƙungiyar Ƙwallon Ƙafa ta Ghana ta kuma ce, “Otto ya nuna hazaƙa yayin tattaunawa da shi, kuma kwamitin neman sabon kocin ƙasar ya ba shi babban maki, shi ya sa aka yanke hukuncin ɗaukar sa”.

Addo ya faɗa a sanarwa daga Dortmund cewa, “Damar karɓar aikin horar da tawagar ƙasata abin alfahari ne”.

Ya ƙara da cewa, “A matsayina na kocin wucin-gadi a baya, na taɓa samun damar ƙwarewa sosai kan wannan aiki. Don haka ina farin cikin karɓar wannan aikin da ke gabana, a bazara mai zuwa.”

Koci mai nemo 'yan wasa

A yanzu, aikin Addo a Dortmund shi ne, "nemo 'yan wasa", wanda ke tattaro zaɓaɓɓun matasan 'yan wasa, a kulob ɗin da ya yi suna wajen samar da fitattun matasan 'yan wasa a Turai. Ya yi aiki da 'yan wasa kamar su Erling Haaland da Jadon Sancho.

Kulob ɗin na Jamus, ya ce ya amince da sakin Addo daga kwantiraginsa a ƙarshen kakar bana, amma kuma za a bar shi ya karɓi ragamar tawagar Ghana a wasannin sada-zumunta na wannan watan.

A baya Dortmund ta taɓa barin Addo ya haɗa aikinsa da na jagorancin tawagar Ghana na wucin-gadi, a shekarar 2022.

An haifi Addo a Hamburg ta Jamus, kuma lokacin yana ɗan wasa, ya ci kofin Bundesliga tare da Dortmund, sannan ya buga wa tawagar Ghana a Kofin Duniya na 2006.

TRT Afrika