Shugaban Kasar Laberiya George Weah ya rubuta wa shahararren dan wasan Najeriya Victor Osimhen (wanda yake wasa a kungiyar Napoli da ke kasar Italiya) wasika, inda ya taya shi murna dangane da tarihin da ya kafa a Gasar Serie A.
Dan wasan ya ci kwallonsa ta 47 a kakar bana a lig din Seria A a wasunsu Fiorentina ranar Lahadi, hakan ya sa Osimhen ya zama dan kwallon Afirka da ya fi yawan kwallaye a tarihin lig din Italiya.
Kuma hakan yana nufin ya sha gaban yawan kwallayen da Shugaban Laberiya George Weah ya zura a lokacinsa.
Shugaba Weah tsohon dan wasan kwallon kafa ne da ya taba taka leda a Italiya, wanda kuma shi ne dan wasan Afirka daya tilo da ya taba lashe kyautar Gwarzon Dan Kwallon Kafar Duniya.
"Alkaluma sun nuna cewa bayan kwallon da ka zura a ranar Lahadi 7 ga watan Mayun bana, a wasanku da Fiorentina, hakan ya sa ka zama dan wasan Afirka da ya fi yawan kwallaye a tarihin Gasar Serie A - wato yawan kwallayenka sun wuce kwallaye 46 da na zura," in ji Shugaban Laberiya.
Har ila yau Shugaba Weah ya ce yana alfahari sosai da Osimhen kuma yana taya shi murna ga wannan nasarar tasa, wadda ya ce, ya same ta ne saboda kwazonsa da aiki tukuru da kuma sadaukar da kansa.
"Na ji dadin kyawawan kalaman da ka yi game da ni bayan da ka samu wannan nasara. Da wannan nake ba ka shawara da kada ka yi kasa a gwiwa saboda akwai wasu sauran manyan nasarorin da na samu wadanda nake fatan kai ma ka same su, kai har ma ka wuce su," in ji shi.