Ranar 22 ga watan Mayu ne za a buga wasan ƙarshe na gasar Europa ta bana. / Hoto: AFP

Bayan kammala wasanni makon nan na Gasar Cin Kofin Zakarun Turai ta UEFA a daren Laraba, hankali ya koma kan gasar Europa, inda ita ma za a kammala zagayen farko na rukunin ƙungiyoyi 16 na gasar a daren Alhamis.

Tun bayan da ƙungiyar Sevilla ta Sifaniya ta gaza shiga gasar Europa ta bana, bayan an fitar da ita a matakin rukuni a gasar Zakarun Turai, manyan ƙungiyoyi huɗu da ke matakin 'yan 16 a yanzu ake ganin za si iya ɗaukar kofin a bana.

Da ma Sevilla ce ta ci gasar a bara, kuma ita ce take da kambun ƙungiyar da ta fi yawan cin kofin a tarihi, inda ta lashe kofin sau bakwai tun daga kakar 2005/2006. Ga kulob huɗu da ake ganin alamun za su iya lashe gasar.

Liverpool

Liverpool ce ta ɗaya a teburin gasar Firimiya ta Ingila, kuma ta ci wasanninta shida na ƙarshe a duka gasanni. Sau uku tana lashe kofin Europa a baya, baya ga cewa ta taɓa cin babban kofin Zakarun Turai har sau biyar.

A daren Alhamis Liverpool za ta fafata da Sparta Praha ta Czech Republic, wasan da ake ganin ba zai yi wa kulob din wahalar tsallake wa ba.

Masu sharhi suna kallon Liverpool a matsayin ƙungiyar da ta fi ƙarfin damar lashe Europa a bana. Rabon da wani kulob ɗin Ingila ya ci kofin Europa tun shekarar 2019, lokacin da Chelsea ta ci kofin.

Bayer Leverkusen

A kakar bana ƙungiyar Leverkusen ta Jamus tana tsakiyar ganiyarta ƙarƙashin sabon koci Xabi Alonso, inda suke kan gaba a gasar Bundesliga, bayan sun kere wa kulob ɗin da ke biye musu da tazarar maki 10.

Har zuwa yau, Leverkusen bai taɓa yin rashin nasara a wasa ba a gasar ta Bundesliga, kuma sun buga wasanni 34 a jere a duka wasanni ba tare da an yi galaba kansu ba.

A tarihi, Leverkusen sau ɗaya ta taɓa cin kofin na Europa a shekarar 1988, kuma kulob ɗin bai taɓa cin kofin Zakarun Turai ba, duk da dai ya taɓa zuwa na biyu sau ɗaya a gasar a 2002.

AC Milan

Ƙungiyar AC Milan ta Italiya na mataki na uku a teburin Gasar Seria A ta ƙasar, inda Inter ke gabanta da tazarar maki 6 kacal. Milan ce ta uku da masu sharhi ke ganin za ta iya cin kofin Europa na bana.

A tarihi, Milan ce ƙungiyar da ta fi kowace ƙungiya daga Italiya cimma nasarori a fagen ƙwallo a nahiyar Turai. Sau bakwai Milan tana cin kofin Zakarun Turai, inda ita ce ta biyu a jerin ƙungiyoyin da suka fi cin gasar.

Wannan ka iya zama dalilin da ya sa ba ta taɓa cin kofin Europa ba a baya, tun da ba ta faye faɗowa gasar ba.

AS Roma

A bara, tsohon kocin Roma Jose Mourinho ya kai su wasan karshe na gasar ta Europa, amma suka yi rashin nasara bayan an kai matakin bugun daga kai sai mai tsaron gida.

Duk da cewa ba su taɓa cin kofin na Europa ba, balle ne Zakarun Turai, tsohon kocin nasu ya ci musu kofin UEFA Conference Cup a shekarar da aka ƙaddamar da shi, wato 2022.

Roma tana mataki na biyar a gasar Serie A ta Italiya, amma tun bayan tafiyar tshohon kocin nasu, kulob ɗin ya samu tagomashin cin wasanninsu hudu cikin biyar na baya-bayan nan a duka gasanni.

TRT Afrika