Shahararren dan wasan AC Milan Zlatan Ibrahimovic ya sanar da yin ritaya daga kwallon kafa yana da shekara 41.
Dan kasar Sweden ya bayyana wa masoyansa a San Siro bayan wasansu na karshe a kakar wasa ta bana ranar Lahadi cewa "Ina yin bankwana da kwallon kafa amma ba bankwana da ku ba."
Ya ci kwallaye 511 a tarihinsa na kwallon kafa a kungiyoyin Paris St-Germain, Manchester United, Barcelona, AC da kuma Inter Milan, inda ya lashe gasa daban-daban a kasashe hudu da ya murza leda.
Ibrahimovic ya koma AC Milan karo na biyu a farkon 2020, bayan ya lashe Scudetto tare da su a 2011, sannan ya sake taimaka musu wurin lashe kofin a kakar wasan da ta gabata.
Ibrahimovic ya soma sana'arsa ta kwallon kafa a kungiyar Malmo FF ta kasarsa a 1999 sannan daga bisani ya tafi Ajax a 2001 inda ya kwashe shekara uku kuma ya lashe kofuna uku.
Dan wasan ya shafe kakar wasa daya kacal a Catalan, inda ya lashe gasar La Liga kafin a ba da aronsa ga AC Milan, kuma daga bisani ya sanya hannu a kan kwantaragin dindindin a 2011.