Vinicius na cikin jerin 'yan wasan da ake ganin za su lashe kyautar gwarzon ƙwallon ƙafa na duniya a bana. / Hoto: AFP

Gwaraza kuma matasan 'yan wasan Brazil, Vinicius Jr da Rodrygo sun gaza taɓuka abin a zo a gani a wasan ƙasarsu na farko a gasar Copa America, inda aka tashi wasa babu wanda ya iya zura ƙwallo a kowace raga.

Gabanin wasan, ba a zaci tawagar Costa Rica da ake wa laƙabi da Los Ticos za ta ba wa tawagar Brazil da ake kira da Selecao mamaki ba, kasancewar Brazil ake wa kallon dandalin haziƙan 'yan wasan ƙwallon ƙafa tun a tarihi.

Hasali ma baya ga cewa Brazil ce ƙasar gawurtattun 'yan wasa irinsu Zico da Pele da Ronaldo Nazario da Neymar Jr, a kakar gasar Copa America ta bana Brazil ce ɗaya cikin ƙasashe biyun da ake ganin za su ɗaga kofin.

A yayin wasan da aka buga a safiyar Litinin a filin wasa na SoFi da ke birnin Los Angeles na jihar California, babu ɗaya cikin jaruman 'yan wasan Brazil, Vinicius da Rodrygo, da ya iya kai bara kan ragar abokan hamayya ko da sau guda.

A ƙarshe dai shi kansa sabon kocin Brazil wanda ya jagoranci wasan, Dorival Junior bai nuna alamun shawo kan wasan ba har aka tashi babu ci.

A yanzu dai ya rage wa tawagar ta Brazil ta shirya wa wasan gaba da Paraguay ranar Asabar, don ganin ta gano bakin zaren, musamman ganin manyan ƙasashe irinsu Argentina da Uruguay tuni sun kammale maki ukunsa daga wasanninsu na farko.

TRT Afrika da abokan hulda