Shahararren kulob din kwallon kafa na Sifaniya, wato Real Madrid, ya samu nasarar kai wa wasan karshen na kofin kalubale na Sifaniya, Copa del Rey a daren Laraba.
Hakan ya faru ne bayan lallasa babban abokin hamayyar Real Madrid din, wato Barcelona, da ci hudu da nema. Wasan Laraban shi ne zango na biyu a wasan kusa da na karshe na cin kofin kasa na Copa del Rey.
Wasan ya wakana ne a filin kwallo na Barcelona da ke Camp Nou. Nasarar ta Real Madrid ta sa kulob din wanda shi ne na biyu a teburin La Liga, ya samu damar buga wasan karshe na kofin Copa del Rey.
Gwarzon dan kwallo da ke zaman na biyu wajen zura kwallaye a La Ligar kakar bana, wato Kareem Benzema shi ya zura kwallaye har uku a ragar Barcelona, yayin da kafin nan matashin dan kwallo nan Vinicius Jr ya fara zura kwallo daya cikin minti na 45.
An tashi wasan ne ba tare da Barcelona ta iya rama ko da kwallo daya ba, inda a karshe gamammen sakamakon zango biyu na wasan ya nuna Real Madrid tana da kwallo hudu Barcelona tana kwallo daya.
Wasan ya bayar da mamaki, kasancewar a zangon farko na wasan a watan da ya gabata, Barcelona ce ta je har gida ta doke Real Madrid da ci daya da nema, a filin kwallo na Santiago Bernabéu da ke birnin Madrid.
A halin yanzu dai an yi waje da Barcelona daga kofin Copa del Rey. Amma dai ita Barcelonan ce ke ci gaba da zama kan gaba a teburin La Liga.
Manajan kulob din, Xavi Hernández yana fatan cin gasar La Liga a karon farko tun bayan zamansa jagorar kungiyar a shekarar 2021.