Real Madrid ta yanki tikitin wasan dab da na karshe a gasar Zakarun Turai ta UEFA, bayan karasa murkushe Chelsea a zango na biyu na wasansu, wanda ya kammala jiya a Stanford Bridge.
Matashin nan mai shekara 22, Rodrygo, dan asalin Brazil shi ne ya ciyo wa Madrid kwallaye biyu a minti na 58 da 80, inda aka tashi wasan Madrid tana da ci biyu Chelsea tana nema (a jimlace, Madrid ta ci hudu, Chelsea ba ko daya).
Rodrygo ya fada bayan kammala wasan cewa, “Ina da wani nasibi na musamman a gasar Zakarun Turai”. Matashin bai yi karya ba saboda ko a kakar bara, shi ne ya kai Madrid wasan karshe bayan cin kwallaye biyu a minti 3 a wasansu da Man City.
Idan ya halatta a gasar Zakarun Turai a kira Real Madrid ‘masu-abin’, to kuwa za a iya yi wa Rodrygo kirari da ‘karaminsu babbansu’.
Tun kafin a kare wasan, gwiwoyin masoyan Chelsea suka yi sanyi, inda suka ringa ficewa daga filin wasan. Alkalin wasa yana busa usur din karshen wasan, sai sauran ‘yan kallon na Chelsea suka fara ihu na nuna takaici.
A fili za a iya cewa wasan ya ba da mamaki, saboda Chelsea ta yi abin a yaba, inda ta fi rike kwallo da 54%, kuma Kante da Cucurella sun kai munanan hare-hare ragar Madrid.
Sai dai mai fashin baki Alejandro Moreno, ya fada wa ESPN cewa, “Ko me za ka ce kan kokarin ‘yan wasan Chelsea, babu daya cikinsu da ya yi kusa da inganci ko karfin zuciya irin na ‘yan wasan Madrid.”
Ita kuwa Chelsea wannan rashin nasara ta kawo karshen yunkurinta na cin kofin turai a wannan kakar. Sannan kuma, rashin nasarar ta zamo ta hudu a jere da ta yi a karon farko tun shekarar 1993.
Haka nan manajansu, Frank Lampard ya zamo koci na farko a Chelsea, wanda bai ci wasa ko daya ba a jerin wasanni hudu da ya jagoranta a matsayin sabon koci a duk Ingila.
Siradin Man City (ko Bayern Munich)
A yanzu dai, Madrid ta wuce zuwa wasan dab da na karshe, kuma za ta tsumayi wasa tsakanin Manchester City da Bayern Munich don sanin da wa za ta kara a gaba.
Hakan na nufin Madrid sun cimma kaiwa wasan dab da na karshe a gasar Zakarun Turai har sau 11 a shekaru 13 na baya-bayan nan. Kuma Madrid din ne ke rike da kofin na UEFA, kuma su suka fi kowa yawan lashe shi har sau 14.
Za a iya cewa siradi guda daya ya rage wa Real Madrid ta tsallaka, wato karawarsu ta gaba da Man City ko Bayern. Idan suka iya yin nasara a zagayen dab da na karshe, za su hadu da daya cikin kulob uku ne, a wasan karshe.
Kungiyoyin da Madrid za ta iya karo da su, su ne AC Milan da Inter Milan na Italiya, ko SL Benfica ta Portugal. Amma bisa tarihin kididdigar nasara, duka ukun nan ba gamin Real Madrid ba ne.
Wato ba za su mata wata barazanar a zo a gani ba. Hasali ma, masu sharhi suna ganin Madrid ta mayar da gasar ta UEFA tamkar wani dausayi da take zuwa duk shekara don shakatawa.
A turance suna kiran abin da “love affair”, wato “alakar masoya”, inda Madrid take soyayya da hamshakin kofin na UEFA. A yanzu ma, Madrid tana fafutukar lashe kofin ne a karo na 15.
Wata kididdiga ta nuna cewa yan wasa uku cikin biyar da suka fi buga gasar Zakarun Turai, wato Cristiano Ronaldo da Karim Benzema da Iker Casillas, duka a Madrid suka cimma wannan bajinta.
A yanzu dai za a saurari wasan yau Laraba don sanin ko Manchester City ko Bayern Munich ne za su zamo babban siradin da Madrid za ta fuskanta, kafin lashe gasar Zakarun Turai ta 2022/23.
A ranar Asabar, 10 ga watan Yuni mai zuwa ne za a buga wasan karshe na gasar ne a filin wasa na Atatürk Olympic Stadium, da ke birnin Istanbul na Turkiyya.