Ana iya kaiwa wata takwas zuwa 10 kafin a warke daga tsagewar kashi ko karaya. / Hoto: AP

Neymar ya soma samun sauki bayan tiyatar da aka yi masa a gwiwa sai dai har yanzu likitoci bayyana takamaiman lokacin da dan wasan kungiyar Al-Hilal zai koma taka leda ba.

Dan wasan, mai shekaru 31, ya samu karaya da tsagewar kashi a sawun gwiwar kafarsa ta hagu a lokacin da yake taka leda wa Brazil a wasan neman gurbin shiga gasar cin kofin duniya na 2026 a watan jiya.

Ana iya kaiwa wata takwas zuwa 10 kafin a warke daga tsagewar kashi ko karaya.

Dokta Rodrigo Lasmar, likitan kungiyar kwallon kafa ta Brazil, ya ce Neymar na iya kokarinsa wajen ganin ya samu cikakkiyar lafiya.

"Tun da farko ya nuna jajircewarsa, wajen bin ka'idojn da muka shimfida masa," Lasmar ya shaida wa wani taron manema labarai a Sao Paulo a ranar Litinin.

An fitar da Neymar daga filin wasa cikin hawaye a kan gadon daukar marasa lafiya yayin wasa tsakanin kasarsa Brazil da Uruguay inda aka tashi da ci 2- 0.

Ya koma kungiyar Al-Hilal ta Saudiyya a lokacin bazara daga Paris St-Germain a kan Yuro miliyan 90, sai dai tun daga lokacin wasanni biyar kawai ya iya buga wa kungiyar sakamakon raunin da ya ji a gwiwarsa.

TRT Afrika