Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Galatasaray da ke Turkiyya ta lashe gasar Super Lig karo na 24 bayan ta doke takwararta ta Tumosan Konyaspor da ci 3 -1 a fafatawar da suka yi ranar Lahadi.
Galatasaray ta jefa ƙwallon farko a minti na 29 inda ɗan wasan Argentina Mauro Icardi ya zura ƙwallon da ka a ragar mai tsaron gida ƙan ƙasar Polan Jakup Slowik. Derrivk Kohn ɗan ƙasar Jamus ne ya taimaka masa.
A minti na 51 Icardi ya ƙara ƙwallo ɗaya a ragar baƙin nasu, bayan Lucas Torreira ya ba shi fas. Bayan 'yan mintuna kuma ɗan wasan tsakiya na Galatasaray Berkan Kutlu ya ƙara ƙwallo ta uku a ragar Konyaspor.
Louka Prip, ɗan ƙasar Denmark da ke taka leda a Konyaspor ya ci wa ƙungiyarsa ƙwallo ɗaya a minti na 71, inda wasan ya koma 3 - 1.
Galatasaray ta yi nasarar lashe gasar Zakarun Turkiyya ta 2024 da maki 102.
Bayan tashi daga wasan, 'yan wasa da shugabannin ƙungiyar sun yi murna har da tsalle.
Kungiyar Fenerbahce ce ta zo ta biyu a gasar inda ta doke Istanbulspor da ci 6 - 0, inda ta kammala gasar ta Suoer Lig da maki 99.
Tumosan Konyaspor ce ta 16 da maki 41 inda za ta sake shiga gasar a kakar wasanni mai zuwa.