Kungiyar kwallon kafar Galatasaray da ke Turkiyya tana tattaunawa da dan kasar Ivory Coast Wilfried Zaha don daukarsa.
Tsohon dan wasan na Crystal Palace, mai shekara 30, ba shi da kungiya tun bayan kwangilarsa ta kare da Palace a karshen watan jiya.
Bayanai sun ce Palace ta yi tayin biyan Zaha £200,000 duk mako domin ya ci gaba da murza leda.
Sai dai a wani sakon da ta wallafa a Twitter, Galatasaray ta tabbatar da cewa ta "soma tattaunawa a hukumance" da dan wasan.
Kazalika ana alakanta shi da kungiyar Lazio ta Italiya, da Al-Nassr ta Saudiyya da kuma Fenerbahce da ke Turkiyya.
Zaha ya zura kwallo 90 a wasanni 458 da ya buga wa Palace, tun da ya tafi kungiyar yana dan shekara 12.
TRT Afrika