Galatasaray ta kafa tarihi inda ta je har gidan Manchester United ta yi nasara. / Hoto: Reuters

Galatasaray ta kasar Turkiyya ta kafa tarihi bayan ta bi Manchester United har gida ta doke ta da ci 3-2 a Gasar Zakarun Turai da suka fafata a Old Trafford.

A karon farko a tarihinta, kungiyar da ke birnin Istanbul ta je kasar Turai ta yi nasara a wasa ranar Talata.

Manchester United ta soma zura kwallo ta hannu Rasmus Hojlund inda ya zura kwallon da ka bayan golan Galatasaray Fernando Muslera ya kasa katabus a minti 17 da soma wasa.

Sai dai nan da nan Galatasaray ta mayar da martani.

Wilfried Zaha, tsohon dan wasan Man United, ya yi amfani da karfinsa a kan Diogo Dalot a kusa da raga inda ya dirka kwallon ta shiga ciki.

Kungiyoyin biyu suna da ci 1-1 kafin a tafi hutu rabin lokaci.

Dan kasar Denmark Hojlund ya ci wa Man Utd a minti na 59, sai dai an hana su saboda bai bi ka'ida ba.

Amma a minti na 67, Hojlund ya sake ci wa Man United wadda aka amince da ita.

Galatasaray ta sake cin kwallo ta hannu dan wasan gaba Kerem Akturkoglu bayan Baris Alper Yilmaz ya mika masa ita.

Kazalika dan kasar Argentina Mauro Icardi ya ci wa Galatasaray kwallo ta uku inda suka tashi 3-2.

TRT Afrika da abokan hulda