Mauro Icardi  zai rika samun €6m duk kakar wasa./Hoto:AA

Kungiyar kwallon kafar Galatasaray ta kasar Turkiyya ta sanar da daukar dan wasan Ajentina Mauro Icardi daga Paris Saint-Germain (PSG) a kan €10m (fiye da $11m).

A sanarwar da ta fitar ranar Lahadi, kungiyar da ke Istanbul za ta kwashe kakar wasa hudu tana biyan kudin ga tsohuwar kungiyar Icardi.

Daga kakar 2023-2024, Icardi zai kwashe kakar wasa uku yana murza leda a Galatasaray. Fitaccen dan wasan zai rika samun €6m duk kakar wasa bayan an cire haraji.

Icardi, mai shekara 30, ya isa filin jirgin saman Ataturk da ke Istanbul ranar Juma'a da maraice inda magoya bayansa suka rika yi masa lale marhabin suna kiran sunansa.

Ya kwashe kakar wasa ta 2022-2023 a Galatasaray yana zaman aro kuma ya ci kwallo 23 a wasanni 26 da ya fafata, inda ya ci gasar Turkish Super Lig.

AA