Filin wasa na Camp Nou da ke Sifaniya yana daukar mutane har 99.354. / Hoto: AP

A shekarar 2023, filin wasan kwallon kafa da aka shiga don kallon kwallo a duniya shi ne Camp Nou, wato filin wasa na Barcelona, inda 'yan kallo 83,273 suke shiga kallo duk wasan Barca na gida, bisa matsakaicin adadi.

Filayen wasan kwallon kafa 16 a duniya da suka fi tara 'yan kallo, duka suna nahiyar Turai ne. Uku suna Jamus sannan uku suna birnin Landan shi kadai.

Kasar da ta fi yawan kungiyoyin kwallo a jerin ita ce Jamus wadda take da kulob 12 da ke buga wasa a matakan kwararru biyu na kasar.

Wadda ke biye mata ita ce Ingila, da kulob 11, sai Sifaniya mai kulob 7 da Italiya mai kulob 6. A kididdigar kasashe 14 suka shiga jerin manyan filayen wasa a yawan masu kallo.

Babban kulob da ke kan-gaba amma wanda ke wajen Turai shi ne filin wasa na kungiyar Flamengo ta Brazil, wadda take mataki na 17 a duniya, kuma take da adadin 'yan kallo 56,689 duk wasa a shekarar ta 2023.

Shafin Transfer Markt ya wallafa wannan kididdiga da ta nuna cewa a nahiyar Arewacin Amurka kungiyar Atlanta United tana da 'yan kallo 47,526 a wasanninta na gida, wanda ya ba ta mataki na 30 a jerin.

Kasar Sifaniya tana da filaye bakwai da ke cikin jerin, amma kulob shida ne ka da filayen. Wannan ya faru ne saboda Bercalona ta shafe rabin shekara tana buga wasa a filin ta na Camp Nou, yayin da sauran ta buga wasanni a babban filin wasan Olympic lokacin da ake gyare-gyare a gidanta.

A Asiya kuwa kulob din kasar China mai suna Bejing Guoan bayan da suka sami 'yan kallo 43,769 duk wasansu na gida.

TRT Afrika