Sifaniya ta zama kungiyar kwallon kafar mata ta biyar da ta yi nasarar lashe gasar Cin Kofin Duniya ta Mata.
Sifaniya ta yi nasarar doke Ingila da ci 1-0 a filin wasa na Australia a ranar Lahadi.
Sifaniya ta ci kwallon ne a minti na 29 inda ‘yar Real Madrid din nan Olga Carmona ta ci wasan.
Sifaniya ta fi Ingila rike kwallo a zangon farko kafin a tafi hutun rabin lokaci.
Ko da aka je hutun rabin lokaci, Sifaniya na da kaso 64 cikin 100 na rike kwallo inda Ingila ke da kaso 36 cikin 100.
Sa’annan Sifaniya ta auna golan Ingila sau biyar ita kuma Ingila ta auna golan Sifaniya sau uku.
Sau hudu Amurka na lashe gasar kwallon kafa ta mata ta duniya sai Jamus sau biyu. Japan ta lashe sau daya haka Norway ma sau daya sai a halin yanzu Sifaniya ta lashe.