Keftin din kungiyar kwallon kafa ta Falasdinu Musab Al-Battat ya bayyana cewa kungiyarsa ta “cika alkawarin da ta dauka ga Falasdinawa” bayan ta kai zagayen sili-daya-kwale a Gasar Cin Kofin Nahiyar Asia a karon farko.
Wasan wanda aka tashi 3-0 wanda suka buga da Hong Kong a ranar Talata shi ne wasa na farko da suka fara ci a gasar kuma ya kai su matakin ƴan 16 a matsayin daya daga cikin huɗu mafi kyau.
Oday Dabbagh shi ne ya kasance gwarzo a Doha inda ya zura kwallaye biyu, sai kuma a usur ɗin ƙarshe da aka busa, sai ƴan wasan Falasdunawa da ma’aikata suka rinƙa mutrna a fili tare da runugmar juna da ɗaga tutoci.
Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa ta zo ta biyu a rukunin C duk da cewa ta yi rashin nasara a ci 2-1 a Iran.
Nasarar da Falasdinu ta samu a kwallon kafa na zuwa ne a daidai lokacin da Isra’ila ke ci gaba da kai mata hare-hare da kuma yin ƙawanya a Gaza.
Ƴan wasa da ma’aikata sun rasa masoyansu sakamakon hare-haren Isra’ila. “Ina so na gode wa duk wadanda suka ba mu goyon baya, "in ji shi.
"Mun yi nasarar sanya murmushi a fuskokin wadanda ke bin mu ... ciki ko wajen Falasdinu. Kafin a soma wasan, an yi ta yin ihun “a ba Falasdinawa ‘yanci”.