Daga Abdulwasiu Hassan
A kwallon kafa, kamar yadda rayuwa take, tabbaci yana da amfani. Kuma mene ne zai fi zama babbar shaida ga irin farin cikin wasan da ake yi fiye da yadda ake neman ‘yan wasa a kungiyoyi.
Magoya bayan Nijeriya da ke sha'awar gasar cikin gida na ci gaba yin fatan ganin an dawo da martabar kwallon kafar kasar - lokaci da suka ga yadda filin wasa na Mobolaji Johnson, wanda aka fi sani da Onikan Stadium, ya cika makil da jama’a a wasan karshe na gasar Naija Super 8 a makonnin da suka gabata
“Wa ya ce gasar kwallon kafarmu ba za ta yi kasuwa ba, in ji wani magoyin baya kwallon kafa.
Yadda filin wasa ya cika makil a gasar da aka buga a ranar 16 ga watan Yuli tsakanin Sporting Lagos da Remo Stars ya kasance wani abu da ‘yan Nijeriya suka dade suna jira.
Sun san cewa gasar kwallon kafa ta cikin gida na da mabiya – batu ne kawai na tabbatar da komai ya tafi daidai.
Sporting Lagos ta doke Remo Stars a bugun daga kai sai mai tsaron gida domin zama zakaran gasar Naija Super 8 a ranar.
Naija Super 8 gasa ce da ake yin ta a lokacin hutun kaka a Nijeriya, “wadda aka kirkiro domin dawo da jin dadi da walwala a gasar cikin gida da kuma saka sha'awar motsa jiki don ciyar da wasan gaba zuwa matsayi mafi girma," in ji masu shirya gasar.
Lokacin da ake kan ganiya
Akwai lokutan da kungiyoyin kwallon kafa na Nijeriya ke da karfi da har suke bai wa babban kungiyar kasar ‘yan wasa nagartattu wadanda suke wasa a gasa daban-daban kamar ta cin Kofin Afirka da kuma ta Kofin Duniya.
Karfin gasar ta cikin gida har ya sa masoya gasar na bin lamarin sau da kafa. Ba wai suna cika filin wasa kadai ba ne a duk lokacin da kungiyoyinsu ke buga wasa, suna kuma bin su duk inda za su buga wasa.
Irin nasarar da gasar cikin gida ta samu a shekarun baya ya yi tasiri a babbar kungiyar kwallon kafa ta kasar, inda kungiyar ta Super Eagles ta kai mataki na koli na hukumar FIFA a 1994 – ta zama ta biyar a duniya sannan ta 1 a Afirka.
A tsawon shekaru, karfin da gasar ta cikin gida take da shi na samar da ‘yan wasa kamar ga kungiyar Super Eagles kamar su Segun Odegbami da Daniel Amokachi da Jay-Jay Okocha da Kanu Nwakwo da Osaze Odemwingie yana ta raguwa.
Aikin kula da sa ido
“Karfin da gwamnati ke da shi wurin mallakar kungiyar kwallon kafa babbar matsala ce,” kamar yadda David Ngobua, editan wasanni na jaridar Daily Trust, ya shaida wa TRT Afrika.
“Bai kamata a ce haka lamarin yake ba, saboda a sauran kasashen da ake buga kwallo a matsayin da kyau, gwamnatoci ba su da wata alaka da daukar nauyi ko kuma kafa kungiyoyi kamar yadda muke yi a Nijeriya.”
“Alal misali, idan muka dubi babbar kungiyar kwallon kafa ta Nijeriya a halin yanzu, kungiyoyi uku ne kacal da za su fafata a gasar ta NPLF a kaka mai zuwa ba na gwamnati ba. Sauran duk mallakar gwamnatocin jihohi ne,” in ji shi.
Zargin kuma da ake yi na rashin adalci wurin alkalancin wasa da kuma rashin tsaro a wurin kallo sun sa magoya bayan kwallon da ‘yan kallo suka gaji da lamarin.
Kafin wasan karshe na gasar Naija Super 8, akasarin wasannin da ake yi babu ‘yan kallo sosai inda wannan da aka yi aka gan su da yawa.
Karancin ra’ayi na jama’a masu biyan haraji na hana kulob-kulob samun kudin shigar da ya kamata su samu daga daga yarjejeniyoyi na watsa wasan a kafafen watsa labarai da kuma kayayyaki da kudin da ake samu na daga shiga a buga wasa. Abin da hakan ke nufi shi ne ana hana tattalin arzikin kasa damar cin gajiyar wadannan abubuwa.
Kwatanta kai da Turai
Masana na ganin gasar kwallon kafa ta cikin gida za ta yi matukar amfana da habaka daga tsarin tattalin arzikin da kowa zai iya zuba jari inda akasarin masu kungiyoyi za su kasance mutane ne masu zaman kansu ko kuma kungiyoyi.
“Ya kamata a ce kamfanoni masu zaman kansu ne ke mallakar kungiyoyin kwallon kafa. Sun fi samun nasara idan haka ta kasance,” in ji Ngobua.
A lokacin da aka soma kwallo a matsayin sana’a a Nijeriya, kungiyoyi kamar su Leventis United da Ranchers Bees na Kaduna da BBC Lions na Gboko da Udoji United da Nwayanwu Nationale duk sun yi kokari.
Kamar yadda Ngobua ya bayyana, duk da cewa wadanda suka je zagaye na karshe a gasar Naija Super 8 da suka hada da Sporting Lagos da Remo Stars – duka ba mallakar gwamnati ba ne kuma sun nuna nasarorin da kungiyoyi za su iya samu idan suna hannun masu zaman kansu.