Carney Chukwuemeka mai shekaru 21 ya zo Chelsea a Agustan 2022. / Hoto: AFP

Ɗan wasan tsakiya na Chelsea, Carney Chukwuemeka, ya fara tattaunawa kan tafiya aro a kasuwar cinikin 'yan wasa ta Janairun nan.

Rahotanni na cewa a 'yanzu Borussia Dortmund ta Jamus ta ƙaddamar da tattaunawa kai-tsaye da Chelsea a ƙoƙarin samun ɗan wasan.

Shafin Goal ya ambato Sky Germany na cewa Dortmund na kallon ɗan wasan mai shekaru 21 a matsayin wanda ya fi dacewa da ya buga musu lamba 8.

Rahotannin sun ce zai tafi ne a matsayin aro, amma tare da zaɓin sayarwa a nan gaba.

A ɓangaren Chelsea, farashin ɗan wasan zai kai dala miliyan $36 zuwa dala miliyan $41.

Baya ga Chukwuemeka, Dortmund na son ɗauko Renato Veiga mai tsaron baya na Chelsea. Veiga ya je Chelsea ne daga FC Basel watanni shida da suka gabata.

Ita dai Chelsea na da burin ba da ɗan wasan a matsayin dindindin, kuma za su nemi farashin da ya kai dala miliyan $36, tare da zaɓin sayarwa.

Kamar yadda kocin Chelsea Enzo Maresca ya faɗa, ƙungiyar na da burin sakin tarin 'yan wasan da ba su samun damar wasa a watan nan na Janairu.

TRT Afrika