Tawagar Chris Harper ta ce zai huta zuwa gaba. Hoto: Reuters    

Chris Harper ɗan asalin ƙasar Austrlia ya janye daga gasar tseren keke na 'Tour de France' gabanni kai wa mataki na 16 a gasar a ranar Talata, a cewar ƙungiyarsa.

Matakin ya biyo bayan ɗaɗa samun masu kamuwa da cutar Covid-19 a cikin 'yan wasa tseren keken.

Ƙungiyar Jayco Alula ta ce Harper "yana fama da wasu alamu na cutar COVID, kuma bisa ga shawarar likita, zai koma gida don samun hutu kana ya murmure yadda ya kamata don shirin gasar na gaba."

Janyewar da Harper ya yi a gasar ya biyo bayan sabbin rahotanni da aka samu kan wasu manyan 'yan wasan da suka kamu da cutar Covid-19 a cikin makonni uku, daga cikin su har da babban abokin karawar Juan Ayuso wato Tadej Pogacar, da Tom Pidcock da kuma Maxim Van Gills.

Masu shirya gasar Tour de France sun sake ɓullo da matakan kariya daga kamuwa da cutar, ciki har da sanye takunkumin rufe fuska ga duk wadanda za su haɗu da 'yan wasan da ma'aikatan ƙungiyoyinsu mabam-banta yayin gasar tseren.

TRT World