Wasu na ganin komawar Pochettino Chelsea ya dace yayin da wasu ke tunanin bai wannan bai kamata ba a halin da Chelsea take ciki/Hoto:Reuters

Chelsea ta kulla yarjejeniya da tsohon kocin PSG da Tottenham Mauricio Pochettino don mayar da shi sabon kocin Blues.

Zai koma kungiyar a lokacin bazara, yayin da Frank Lampard zai cigaba da kasancewa kocin kungiyar na wucin-gadi zuwa karshen wannan kakar.

Pochettino, wanda ya taba zama kocin Southampton, ya kasance ba shi da aiki tun lokacin da Paris St-Germain ta maye gurbinsa da Christophe Galtier a bazarar 2022.

Dan kasar Ajantina, mai shekara 51, ya jagorancin Spurs na tsawon shekara biyar daga 2014 kuma ya samu ya kai kungiyar wasan karshe na gasar Zakarun Turai na shekarar 2019.

Pochettino ya taba kai Spurs wasa na karshe a Gasar Zakarun Turai a shekarar 2019/Hoto:Reuters

Pochettino zai kasance kocin Chelsea na shida cikin jerin sunayen wadanda aka bai wa kocin din-din-din a kungiyar cikin shekara biyar, bayan an kori Thomas Tuchel da Graham Potter a wannan kakar.

An bai wa Lampard rikon Blues a farkon watan Afrilu bayan an kori Potter.

Chelsea ta sha wahala a wannan kakar, inda ta sha kaye a hannun Manchester City a zagaye na uku na gasar kofin FA da kuma League Cup.

Kazalika kungiyar ta sha kaye a hannun Real Madrid a matakin daf da na kusa da na karshe na Gasar Zakarun Turai, wanda ya kawo karshen fatanta na shiga gasar Turai a kaka mai zuwa.

A halin yanzu Chelsea ce ta 11 a teburin gasar Firimiya, inda ta yi nasara a wasa daya tilo cikin wasanni 11 da ta buga a baya bayan nan, kuma ta sha kaye a cikin takwas daga cikinsu.

Daga Spurs ne Pochettino ya koma PSG/Hoto:Reuters

Tun lokacin da Spurs ta rabu da Antonio Conte a cikin watan Maris ne dai aka alakanta Pochettino da komawa Tottenham.

Ya kai Spurs wasan karshe na gasar League Cup a shekarar 2015 kuma ya kai ga matakita na biyu a teburin gasar Firimiya a kakar 2016-17, inda kunyiyar ta san a rasa gasa biyun, yayin da Chelsea ta lashe su.

Bayan ya yi aiki a Tottenham, Pochettino ya karbe ragamar PSG daga hannun Tuchel a watan Janairun shekarar 2021.

Kungiyar ta kasar Faransa ta kammala gasar Ligue 1 ta kakar 2021-22 a matsayi na biyu a teburin gasar, amma ta lashe gasar Coupe de France da kuma gasar Trophee des Champions, wadanda suka kasance kofuna na farko da Pochettino ya fara samu a aikinsa na koci.

Pochettino ya fara aikin koci ne dai a Espanyol kafin ya yi aikin wata 16 a Southampton.

Tun da ya bar PSG a shekarar 2022 ne dai Pochettino ya kasance ba shi da aikin koci/Hoto:Reuters
TRT Afrika da abokan hulda