A 2018 ne FIFA ta fara bibiyar cinikayyar 'yan wasa mata tsakanin ƙungiyoyin ƙwallo a duniya. / Hoto: AP

Wani rahoto ya ce a shekarar 2024, ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa a ƙasashen duniya sun kafa tarihin kashe kuɗin da ya kai dala biliyan $8.59 wajen sayayyar 'yan wasa na ƙasa-da-ƙasa.

A ranar Alhamis ɗin da ta gabata ne aka saki sabon rahoton na hukumar ƙwallon ƙafa ta duniya, FIFA kan cinikayyar 'yan wasa na 2024.

Rahoton ya ce, "An yi cinikayyar jimillar 'yan wasa 78,742 a 2024 maza da mata ƙwararru da matakin ƙasa da su".

A shekarar 2023 an kashe dala biliyan 9.66, yayin da adadin a shekarar 2024 ya sauka zuwa 8.59, cewar rahoton na FIFA.

Manyan ƙasashe

Rahoton ya ambato Ingila a matsayin ƙasara da aka fi kashe kuɗi a ciniki 'yan wasa, inda aka kashe dala biliyan $1.88, kuma aka samu kuɗn shiga da ya kai dala biliyan $1.34.

"Kusan kashi 40% na kuɗaɗen cinikin a fannin 'yan wasa maza ya samu ne daga kashi 2.5% na manyan cinikin da aka yi, wanda ya haɗa da kuɗin da ya kai aƙalla dala miliyan $20 a duk ciniki".

A cewar rahoton na FIFA, ƙungiyoyin Brazil sun samu mafi yawan adadi 'yan wasa a 2024, inda 'yan wasa 1,102 suka shiga, sannan guda 1,113 suka fita.

"Adadin ƙungiyoyin da suka kashe kuɗi kan sayo 'yan wasa ya ƙaru, inda ya kai ƙungiyoyi 1,100 a 2024. Sannan yawan ƙungiyoyi da suka karɓi kuɗin ciniki ya kai 1,378"

A ɓangaren mata kuwa, a 2024 an yi cinikin 'yan wasa har na dala miliyan $15.6, inda aka ce an samu ƙaruwar kashi 20% cikin shekara ta shida a jere. Kuma ƙungiyoyi 695 ne suka yi cinikayyar.

AA