A kakar bana ne aka fara sabon tsarin buga gasar ta Zakarun Turai. / Hoto: AFP

A Juma'ar nan ne aka fitar da jadawalin wasannin zagayen gaba na Zakarun Turai, a wani biki da ya gudana a birnin Nyon na ƙasar Switzerland, inda hedikwatar hukumar UEFA take.

A zagayen na gaba, ƙungiyoyi biyu za su kara sau biyu don ƙoƙarin neman wucewa gaba, kuma abin da ya fi ɗaukar hankali shi ne sake haɗa ƙungiyoyin Real Madrid da Manchester City a wasa.

Waɗannan zaratan ƙungiyoyi dai su ne suka ci kofin a bara da kuma shekarar da ta gabace ta. Manchester City ce ta lashe kofin a 2023 a birnin Istanbul, yayin da Real Madrid ta ɗaga kofin a 2024 a birnin London.

A sabon tsarin jadawalin gasar bana, Liverpool, Barcelona, Arsenal, Inter Milan, Atletico Madrid, Bayer Leverkusen, Lille, da Aston Villa, su ne ƙungiyoyi takwas da suka zo kangaba, kuma suka wuce zagayen 'yan 16 kai-tsaye.

Ƙungiyoyin da suka zo na 9 zuwa na 16 a tebruin gasara a wasannin zagayen rukuni, an saka su haɗu da ƙungiyoyin da suka zo na 17 zuwa na 24 don neman shiga zagaye na gaba.

Atalanta, Borussia Dortmund, Real Madrid, Bayern Munich, AC Milan, PSV Eindhoven, Paris Saint-Germain, Benfica, Monaco, Brest, Feyenoord, Juventus, Celtic, Manchester City, Sporting Lisbon, da Club Brugge, su ne suka gama a mataki na 9 zuwa 24.

Za a buga wasannin zagayen ƙafa biyu, ƙafar farko a ranakun 11 ko 12 ga Fabrairu. Sannan ƙafa ta biyu za a buga a ranakun 18 ko 19 na Fabrairu. A nan gaba ne za a fitar da ranakun da za a buga kowane wasa.

Ga jerin ƙungiyoyin da za su kara a wasannin:

Club Brugge – Atalanta

Sporting CP - Borussia Dortmund

Manchester City - Real Madrid

Celtic - Bayern Munich

Juventus - PSV

Feyenoord - AC Milan

Brest - Paris Saint-Germain

Monaco - Benfica

AA