Neymar Jr yana da shekaru 32 a duniya. / Hoto: Reuters

Mashahurin ɗan wasa kuma tsohon kyaftin ɗin tawagar ƙasar Brazil, Neymar, ya miƙa saƙon ban-kwana ga masoya ƙungiyar Al Hilal ta Saudiyya, bayan da zamansa a ƙungiyar ya zo ƙarshe.

Ɗan wasan zai koma tsohuwar ƙungiyarsa da ke Brazil, wato Santos, wadda a can ne ya fara buga ƙwallo tun yana matashi, kafin ya koma Barcelona a 2013.

Al wannan makon ne Al-Hilal ta soke kwantiraginsa duk da yana da sauran watanni shida, bayan gazawarsa ta buga musu wasanni sakamakon yawan tafiya doguwar jinya da ya yi ta yi.

A baya an yi ta raɗe-raɗin cewa Neymar zai koma Santos, musamman ganin yadda Al-Hilal ta cire sunansa daga jerin 'yan wasan da za su buga mata ragowar wasannin kakar bana.

Neymar ya wallafa saƙo a Instagram, inda yake cewa, "Ga kowa a Al Hilal, ga masoya, Na gode!! Na ba da duka ƙarfina don ganin na buga wasa kuma na yi fatan a ce zamana a can ya fi haka kyau."

Zaftarewar albashi

Gabanin zuwansa Saudiyya, Neymar wanda ke da shekarunsa 32 a yanzu, ya buga wa manyan ƙungiyoyi kamar Barcelona da PSG, amma a Al-Hilal jinya ta hana shi sukunin buga wasanni.

A bazarar 2023 ne Neymar ya bar Paris Saint-Germain zuwa Al-Hilal kan kuɗin da ya kai a dala miliyan $98, amma sau bakwai kacal ya buga musu wasa a duka gasanni.

Ana kallon wannan kwantiragi a matsayin mafi asara a tarihin cinikin 'yan wasan ƙwallo.

A yanzu dai rahotanni na cewa Neymar ya haƙura da a zaftare albashinsa a Santos, inda zai koma dindindin, maimakon tafiya aro.

TRT Afrika