Manchester City ta ƙare zagayen rukuni tana mataki na 22 a teburin da ke da ƙungiyoyi 36. / Hoto: Reuters

Bayan da aka kammala zagayen rukuni na gasar Zakarun Turai a Larabar makon nan, kocin Manchester City, Pep Guardiola ya yi nuni da 'matsalar' da sabon tsarin gasar ya haifar a bana.

Man City dai ta sha da ƙyar a matakin rukuni, inda sai a wasan makon ƙarshe ta samu shiga sahun ƙungiyoyin da za su ci gaba da buga gasar a mataki na gaba.

City ta ƙare zagayen rukuni tana mataki na 22 a teburin da ke da ƙungiyoyi 36, inda ta ci wasanni 3 kacal cikin 8, sannan ta ƙare da maki 8.

A wasan da aka buga suka buga a gida da Club Brugge, an fara cin su ƙwallo a zagayen farko, kafin da a zagaye na biyu Kovacic da Savinho suka rama ƙwallo guda-guda, tare da ƙwallon da ɗan wasan Brugge ya ci gidansu, inda aka tashi da ci 3-1.

Da yake jawabi ga 'yan jarida, Guardiola ya yabi sabon tsarin gasar saboda ƙayatarwar da ya kawo, amma kuma ya soki wasu 'matsaloli' kamar na ƙaruwar wasannin da kowace ƙunya za ta buga.

Ya kuma yi bayani kan wasan da Man City za ta buga a gaba, inda ake hasashen za ta haɗu da Bayern Munich ko Real Madrid a zagayen siri-ɗaya-ƙwale, inda ya yi kurarin cewa sabbin 'yan wasansa za su taimaka sosai.

Tagomashin Manchester City dai ya yi ƙasa sosai a wannan kaka, inda duk da su ne ke riƙe da kofin gasar Firimiya, a yanzu alamu na nuna kofin ya kufce musu a bana.

Sai dai kuma, tun da sun samu wucewa zagayen gaba a gasar Zakarun Turai, ƙungiyar za ta yi fatan taɓukawa. Sannan akwai kofin gasar FA da har yanzu suke ciki.

TRT Afrika