Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Afirka CAF ta fitar da sabon tambarin Gasar Zakarun Cin Kofin Afirka ta Mata karo na huɗu, wadda za a soma a Maroko a ranar 9 ga watan Nuwamban 2024.
A wata sanarwa da ta fitar a ranar Laraba, ta bayyana cewa sabon tambarin wanda aka fitar mai ɗauke da kofi na alamta "jajircewa da gogewar ƙungiyoyin mata da kuma nuna yadda gasar ke ƙara haɓaka."
Za a bayar da kyautar kuɗi mai tsoka a gasar ta bana inda duk wanda ya yi nasara zai iya samun dalar Amurka 400,000, sai kuma na biyu da zai samu dala 250,000.
CAF ta ce ƙarin kuɗin na nuna "sadaukarwarta na tallafa wa ƙwallon ƙafa ta mata da kuma ƙarfafa 'yan wasa mata a faɗin nahiyar."
Ana sa ran ƙungiyoyi takwas za su fafata a gasar.
Masu riƙe da kofi: Mamelodi Sundowns (Afirka ta Kudu)
Masu masaukin baƙi: ASFAR (Maroko)
WAFU A: Aigles de la Medina (Senegal)
WAFU B: EDO Queens (Nijeriya)
COSAFA: University of the Western Cape (Afirka ta Kudu)
UNAF: FC Masar (Masar)
CECAFA: CBE FC (Ethiopia)
UNIFFAC: TP Mazembe (DR Congo)