Mourinho yana daga cikin masu horas da 'yan wasa wadanda suka yi suna a duniya. / Hoto: Getty Images

Kungiyar kwallon kafa ta AS Roma a ranar Talata ta tabbatar da sallamar kocinta Jose Mourinho.

“AS Roma za ta iya tabbatar da sallamar Jose Mourinho da ma’aikatansa na horaswa inda za su bar kulob din nan take,” kamar yadda kulob din ya tabbatar a wata sanarwa.

“Muna so mu gode wa Jose Mourinho a madadinmu da ke AS Roma kan kokarinsa tun bayan zuwan shi kulob din,” in ji Dan da Ryan Friedkin, wadanda su ne mamallakan kulob din.

“Za mu ci gaba da tuna kyawawan abubuwa game da zamansa a Roma, amma muna da yakinin cewa sauyi nan take shi ne abin da kulob din yake bukata,” kamar yadda suka bayyana, inda suka yi wa Mourinho fatan alkhairi a aikin da ya saka a gaba.

Roma ta nada Mourinho kocin kulob din tun a 2021.

A karkashin jagorancinsa, Roma ta samu nasara a gasar UEFA Europa Conference League.

Kafin komawarsa AS Roma, ya kasance koci a wasu kulob wadanda suka hada da Real Madrid da Chelsea da Manchester United da Tottenham Hotspur.

AA