Manchester City ta ƙara samun tasgaro a ƙoƙarinta na riƙe ragamar teburin Firimiya, inda ta kuma tsira da maki ɗaya a wasan da ta buga da Newcastle a yau Asabar, inda aka tashi 1-1.
A makon jiya ma Man City ta yi canjaras da Arsenal da ci 2-2, wanda ya ba ta damar ci gaba da zama a saman tebur. Haka a makon nan Man City na da maki 14 daga wasanni 6.
Ɗan wasan Newcastle Anthony Gordon ya ci bugun ɗurmen da ya samu a minti na 58, inda ya farke ƙwallon da City ta ci tun a zagayen farko na wasan a minti na 35, ta hannun Josko Gvardiol.
Ana kallon wasan na yau a matsayin koma baya ga City, kuma ana ta'allaƙa hakan da alamun matsala ga tawagar da Pep Guardiola ke jagoranta, musamman bayan rashin ɗan wasan tsakiya Rodri, wanda jinya ta kawo ƙarshen wasansa a kakar bana.
Arsenal ta sha da ƙyar
Hankula sun raja'a kan cewa Arsenal ta haye kan teburin Firimiya bayan da ta ci ƙwallaye biyu a zagayen farko na wasansu da Leicester, inda Gabriel Martinelli ya ci ƙwallo ta farko a minti na 20, sannan Leandro Trossard ya ci ta biyu a minta na 46.
Sai dai tamkar an yi wa Arsenal baki, bayan dawowa daga hutun rabin lokaci, sai ɗan wasan Leicester James Justin ya farke duka ƙwallayen biyu a minti na 47 da na 63, inda wasa ya dawo ɗanye ga Arsenal.
Haka wasa ya ja har zuwa mintin na 90 ana 2-2, har aka fara fitar da rai. Sai dai a minti na huɗu na ƙarin lokaci sai Bukayo Saka ya ɗana wa Trossard ƙwallon da ya zura cikin ragar Leicester. Sannan a minti na 99, Kai Havertz ya zura ta huɗu.
Wannan ya ba wa Arsenal nasarar kammala wasan da ci 4-2, inda kuma ya sanya ta haye teburin gasar tare da Manchester City, wadda ke gabanta a yawan ƙwallaye.
Chelsea ta wanke Brighton
A wani wasa da ya yi matuƙar ƙayatarwa, Chelsea ta yi nasara kan Brighton & Hove Albion da ci 4-2. Matashin ɗan wasa Cole Palmer ne ya ciyo wa Chelsea duka ƙwallaye huɗu a mintuna na 21, 28, 31, da 41. Ƙwallo ɗaya ce kawai ya ci a fenareti, wato a minti 28.
Brighton ce dai ta fara zura ƙwallo tun a minti na 7, ta hannun Georginio Rutter, kafin daga bisani Palmer ya rama wa Arsenal ya kuma ƙara biyu tun kafin a tafi hutun rabin lokaci.
Ba a ƙara wata ƙwallo a zagaye na biyu na wasan ba, inda aka tashi wasan da ci 4-2, wanda hakan ya bai wa Chelsea damar komawa ta uku a teburi, ta haye kan Liverpool, wadda za ta buga wasanta na mako na shida a maraicen yau tare da Wolverhampton.