Naby Keita ya buga wa Liverpool wasa tsawon shekara biyar. / Hoto: AFP

Shafin ƙungiyar Werder Bremen ta Jamus sun goge sunan ɗan wasa ɗan asalin Guinea, wanda ta sayo kan Fam miliyan £48 daga Liverpool. Ana kallon hakan a matsayin ƙoƙarin tursasa wa ɗan wasan ya bar ƙungiyar.

Ana hasashen Keita zai koma buga wasa a gasar Super League ta ƙasar China, a kakar cinikayyar 'yan wasa da za a buɗe a Janairun baɗi.

Keita mai shekaru 29 ya sha fama da ƙalubale a rayuwarsa ta wasa, ciki har da lokacin da ya ƙi buga wa ƙungiyarsa ta Bremen a wasansu da Bayer Leverkusen a Afrilun da ya gabata.

Bremen ta ɗauko shi ne lokacin da kwantiraginsa ta ƙare da Liverpool a kakar 2022. Ya shigo Liverpool ne daga RB Leipzig a 2017.

A yanzu dai Werder Bremen ta cire hoton Naby Keita daga jerin 'yan wasanta da ke shafinta na intanet, kuma abin da ya rage sai sunansa da lambar rigarsa.

Shafin Goal ya ruwaito mujallar Bild kan cewa Bremen ta yi tunanin ta rabu da Keita a Satumba, bayan ya amince da tayin komawa ƙungiyar Hatayspor ta Turkiyya, wanda ya sha alwashin biyan wani kaso na albashin ɗan wasan don kaucewa asara.

Sai dai hakan bai faru ba, saboda Keita ya sauya shawarar barin Jamus duk da amincewar sauya sheƙar, sannan bayan ya yi gwajin lafiya.

Wannan batun ya ƙona wa Bremen rai matuƙa, inda ta yanke hukuncin daina saka Keita cikin tawagarta, har ya koma yin atisaye shi kaɗai.

Tun bayan barin Liverpool a 2022, Keita ya buga jimillar wasanni da ba su wuce biyar ba kacal a Bremen, inda kwantiraginsa ba za ta ƙare ba sai 2026, duk da yana ci wa kulob ɗin kusan Euro €7,000 duk rana.

Bremen na fatan goge hoton Keita zai tursasa masa barin kulob ɗin a hunturu mai zuwa, tun da ya ƙi tafiya a bazarar nan. Yanzu suna fatan ya tafi China, inda ake da ƙungiyoyin da ke sha'awar ɗaukan sa, yayin da tattaunawa ke ci gaba a bayan fage.

TRT Afrika