Ruben Marques Amorim na dab da lashe kofin Primeira Liga na Portugal a karo na biyu tare da Sporting Lisbon / Photo: AFP

Rahotanni sun nuna cewa Ruben Amorim, kocin Sporting Clube de Portugal, wadda aka fi sani da Sporting Lisbon ko Sporting CP da ke Portugal, shi ne zai zama sabon kocin Liverpool.

Bayan da aka ruwaito cewa ƙungiyar Liverpool suna tattaunawa da Amorim domin shirin ba shi ragamar kulob ɗin, shafin Goal.com ya bayyana cewa tuni Amorim ya zayyana 'yan wasa uku da zai so ya taho da su Liverpool idan ya zama jagora a Anfield.

Amorim ya nuna bajinta a jagorancin Sporting Lisbon da ke buga gasar Primeira Liga ta Portugal, inda yake dab da lashe kofin gasar Primeira Liga a karo na biyu, kuma hakan ya janyo hankali manyan ƙungiyoyin Turai ciki har da Liverpool.

Yayin da aka ambato cewa tattaunawarsu ta kusa cimma matsaya, an fara tunanin waɗanne 'yan wasa ne zai ɗauko idan ya dawo Liverpool.

Cikin 'yan wasan da aka ce yana fatan kawo wa Liverpool har da Goncalo Inacio, da Morten Hjulmand, da kuma Ousmane Diomande.

Duka 'yan wasan a yanzu suna buga wa kulob ɗin da Amorim ke jagoranta a Portugal. Goncalo Inacio da Ousmane Diomande 'yan wasan baya ne, yayin da Martin Hjulmand ke zaman ɗan wasan tsakiya.

Inacio da Diomande sun kasance kangaba wajen taimaka wa ƙungiyarsu ta Sporting Lisbon ƙarƙashin Amorim, inda suka zamo katangar baya da ke tsare gidan kulob ɗin.

Da ma Liverpool na fama da matsala a tsaron bayanta, sakamakon jinyar da manyan 'yan wasanta na baya suke, irinsu Ibrahima Konate da Joe Gomez. Don haka ne ake ganin kawo sabbin 'yan wasan baya daga Sporting Lisbon zai taimaka wa Liverpool.

Shi kuwa ɗan wasan tsakiya Hjulmand ɗan asalin Denmark wanda ke da shekaru 24 ya nuna bajinta a zamansa a kulob ɗin, kuma ya ja hankalin ƙungiyoyin Ingila irinsu Tottenham.

Sporting Lisbon ƙarƙashin Ruben Amorim ta samu nasarori a wannan kaka, inda ta ci wasanni 23 cikin 27. Tsarin zuba 'yan wasa a fili na Amorim shi ne 3-4-3, wanda ya saɓa wa tsarin Klopp na 4-3-3.

TRT Afrika