FC Barcelona unveil Dani Alves / Photo: Reuters

Wata kotu a Sifaniya ranar Alhamis ta yanke wa tsohon ɗan wasan Barcelona da Brazil Dani Alves hukuncin ɗaurin shekara huɗu da rabi a kurkuku bayan samunsa da laifin yi wa wata mace fyaɗe a wani gidan rawa a watan Disamba na 2022.

Kazalika kotun ta umarci tsohon gwarzon ɗan wasan ya biya matar diyyar euro 150,000 ($162,000).

"Macen ba ta amince da abin da ya aikata ba, kuma akwai shaidu da suka nuna cewa ya yi mata fyaɗe, baya ga shaidar da ita kanta ta bayar," a cewar hukuncin kotun ta Barcelona.

"Kotun ta yi laakari da saidu da suka nuna cewa mutumin da ake ƙara ya cakumi matarm ya jefar da ita a ƙasa sannan ya yi lalata da ita, inda ya hana ta motsi yayin da take neman ya bar ta."

Masu shigar da ƙara sun nemi kotu ta yanke wa Dani Alves hukuncin ɗaurin shekara tara.

Alves, wanda ya bayar da shaidar cewa ya yi lalata da macen ne bayan ta amince da buƙatarsa, yana iya ɗaukaka ƙara.

TRT Afrika