Ɗan wasan gaban ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Galatasaray Kerem Akturkoglu ya yi Allah wadai kan harin da Isra’ila ta kai asibitin Al-Shifa da ke Gaza.
Ɗan ƙwallon na ƙasar Turkiyya ya soki Isra’ilar a shafinsa na Instagram.
“Me bil’adama ke jira kafin su dakatar da wannan zaluncin da fyaɗe da ta’addancin? Shin kare haƙƙin bil’adama da rayuka da dukiyoyi ya danganta ne kaɗai da wani sashe na duniya?” kamar yadda ya rubuta a ranar Lahadi.
Ya kuma ƙara da cewa “Ya Allah, mu bayinka ne ba mu da ƙarfin dakatar da wannan abin kunyar. Ku taimake mu!”
Haka kuma Akturkoglu ya wallafa wani hoto da ke nuna yadda aka lalata asibitin Al-Shifa.
Akturkoglu, wanda ya soma taka leda a Galatasaray a 2020, ya taimaka wa kulob ɗin samun nasara a gasar Turkish Super Lig a kakar 2022-2023.
'Ramuwar gayya'
Isra’ila ta ƙaddamar da yaƙi kan ƙungiyar Hamas tun bayan da Hamas ɗin ta kai wa Isra’ilar hari inda ƙasar ta ce ta kashe mata kusan mutum 1,200.
Sama da Falasɗinawa 32,200 Isra’ilar ta kashe a hare-haren ramuwar gayya tun bayan nan tare da raunata sama da mutum 74,500.
Yakin Isra'ila ya sa kashi 85% na al'ummar Gaza sun rasa muhallansu da kuma jefa su cikin matsanancin karancin abinci, ruwa mai tsafta da magunguna, yayin da kashi 60% na ababen more rayuwa na yankin suka lalace a cewar Majalisar Dinkin Duniya.