Ɗan ƙwallon Ivory Coast Ndicka baya fama da 'abin da muke tsoro' bayan faɗuwarsa

Ɗan ƙwallon Ivory Coast Ndicka baya fama da 'abin da muke tsoro' bayan faɗuwarsa

An ɗauki hoton Evan Ndicka yana zaune a kan gadonsa na asibiti yana murmushi.
An ɗauki hoton Evan Ndicka yana zaune a kan gadonsa na asibiti yana murmushi. Hoto / Reuters

Dan wasan baya na Roma Evan Ndicka yana "samun sauƙi sosai" bayan ya faɗi a filin wasa a wasan da suka buga da Udinese a Gasar Serie A a ƙarshen makon da ya gabata, in ji kocinsa Daniele De Rossi a ranar Laraba.

Dan wasan na Ivory Coast din mai shekaru 24 ya fadi a ƙasa ne a minti na 70 na wasan na ranar Lahadi, wanda aka yi watsi da shi bayan da Ndicka, wanda ya kasance cikin hayyacinsa, ya bar filin a kan gadon ɗaukar marasa lafiya.

De Rossi ya shaida wa manema labarai cewa "Yana lafiya. Matsalar huhu abu ne mai zafi, amma cikin sa'a, za mu iya cewa, ba ya fama da abin da muka ji wa tsoro lokacin da ya fadi a filin wasa."

Roma a farkon wannan makon ta ce lamarin ba matsalar ciwon zuciya ba ne, kuma an dauki hoton Ndicka yana murmushi yayin da yake zaune a kan gadon asibiti sa'o'i kadan bayan faruwar lamarin.

Sakamakon gwaje-gwaje

Ya kwana a karkashin kulawar likitoci kafin ya koma harkokinsa a Roma, bayan da gwaje-gwajen asibiti ba su nuna alamun matsalar zuciya ba, amma a maimakon haka "an gano wani rauni a tsakanin huhu da ƙirjinsa."

Wasan na ranar Lahadi ya kasance 1-1 lokacin da aka dakatar da shi. Za a buga wasan karshe a nan gaba, wanda har yanzu ba a tabbatar da shi ba.

De Rossi ya ce kiran yin watsi da wasan shi ne kawai yanke shawara mai yuwuwa.

Sakamakon fargabar da aka shiga ta Ndicka, Roma na shirya wani shiri na bayar da gwajin zuciya kyauta ga magoya bayan da suka haura shekaru 45 a wani asibiti a yankin, gabanin wasansu na gaba na gida da Bologna a ranar 22 ga Afrilu.

AFP