Halil Umut Meler yana cikin alkalan wasan UEFA Elite da FIFA da suka busa wasanni da dama na UEFA da kuma gasa daban-daban na cin kofin gida. /Hoto: AA

An tsare shugaban kungiyar kwallon kafa ta MKE Ankaragucu da ke Turkiyya, Faruk Koca, saboda naushin alkalin wasa Halil Umut Meler a fuska bayan wani wasan lig, a cewar ministan shari'a na kasar.

Yılmaz Tunc ya wallafa sako a shafinsa na X ranar Talata da ke cewa wata kotun Ankara ta tsare mutum uku, ciki har da Koca, bayan Ofishin Mai Shigar da Kara ya dauki bayanansu a babban birnin na Turkiyya.

Tunc ya ce an tsare mutanen da ake zargi Faruk Koca, S.Y.S. da K.C. saboda "ji wa jami'in gwamnati rauni a filin kwallo abin da ya sa ya karye" a yayin da Meler, wanda ake kallo a matsayin jami'in gwamnati, yake gudanar da aikinsa a filin kwallon kafa.

Kungiyar ta Ankaragucu wadda ta buga wasa da 'yan kwallo 10 ta tashi da ci 1-1 da kungiyar Caykur Rizespor a fafatawar da suka yi ranar Litinin a Gasar Trendyol Super Lig.

Bayan kammala wasan ne, Koca ya ruga aguje cikin fili ya yi ta naushin Meler a fuska, alkalin wasan da FIFA ta bai wa lasisi. Alkalin wasan ya fadi a kasa, kuma hakan ya sa mutane da dama suka hau kansa da duka. Daga bisani an kai Meler wani asibiti da ke Ankara.

Shugaba Recep Tayyip Erdogan ya yi Allah wadai da kai wa alkalin wasan hari.

"Ina yin tir da harin da aka kai wa alkalin wasa Halil Umut Meler bayan wasa tsakanin MKE Ankaragucu da Caykur Rizespor da aka gudanar da maraicen nan, kuma ina fata zai samu sauki nan ba da jimawa ba," in ji shugaban kasar a sakon da ya wallafa a shafin X.

TRT World