Hukumar 'yan sanda a Ingila ta kori wani ɗan sanda mai goyon bayan Chelsea bayan ya amsa laifin ambata kalaman ƙiyayya a wani wasa da Chelsea ta buga a gidan Liverpool da ke Anfield.
Sergeant Tyler Coppin ya amsa laifin da aka zarge shi wanda ya saɓawa tsarin ɗa'a a bainar jama'a, bayan da aka fitar da shi daga filin wasan Liverpool a Anfield kuma aka kama shi a Oktoban 2024.
Hukumar 'yan sanda ta Essex ta yi bincike a kan batun rashin ɗa'a kan ɗan sandan magoyin bayan Chelsea, wanda ya janyo aka masa hukuncin haramci na shekara uku, tare da tarar fam £645.
Ma'aikatan filin ƙwallo ne suka fitar da Coppin bayan an gan shi yana furta munanan kalamai ga magoya bayan Liverpool.
Bayan nan ne wani kwamitin ladabtarwa ya tabbatar da cewa ɗan-sandan ya "saɓa tsarin halayyar ƙwarewa dangane da nuna gaskiya da riƙon amana, da ɗa'a da mutuntawa”.
Daga nan kuma hukumar 'yan sandan ta Essex ta kori Coppin ba tare da ɓata lokaci ba, kuma ta sanya shi cikin jerin waɗanda aka haramtawa aiki na makarantar 'yan-sanda ta College of Policing.
Duk da cewa a baya ba a taɓa samun sa da rashin ɗa'a ba, a yanzu an kalli abin da ya yi a matsayin “laifin rashin aikata abu mara dacewa” kuma aka masa "hukuncin da ya dace”.
Babban sufeton 'yan-sandan na Merseyside, Kevin Chatterton ya ce, “Irin wannan halayya ba a amincewa da ita a harkar ƙwallo. Za mu ɗauki mataki kuma ma nemo waɗanda suka aikta laifin ƙiyayya a kowane yanayi.”
A cewar hukumar hukunta laifi ta Crown Prosecution Service, laifin da aka yi hukuncin kansa ya shafi “idan masoya tawagar ƙwallo suka yi kalamai, ko alamta saƙonnin tunzurawa game da bala'i ko hatsari kan 'yan wasa ko sauran masoya ƙwallo”.