David Coote, alƙalin wasa ne da ke alƙalanci a wasannin ƙwallo na Ingila, ciki har da na babbar Gasar Firimiya. Sannan yana alƙalanci a Turai inda ya yi aiki a wasu wasannin gasar Euro 2024 da aka yi a farkon 2024.
A makonnin baya ne aka kwarmata wasu bidiyoyi daban-daban da ke nuna David Coote yana wasu abubuwan da hukumar ta ce 'sun saɓa wa dokar ɗaukar sa aiki'.
Wata sanarwa da PGMOL ta fitar yau Litinin, ta tabbatar da sallamar Coote daga aiki, inda ta ce bincikenta ya nuna ba zai yiwu ya ci gaba da aiki ba, don haka ta kore shi yau kuma nan-take.
Ɗaya cikin bidiyoyin ya nuna Coote yana faɗan munanan kalamai kan Liverpool da kuma tsohon kocin ƙungiyar, Jurgen Klopp.
Hukumar ta PGMOL ta ce bayan dakatar da shi lokacin da ta ƙaddamar da bincike kan zarge-zargen, a yanzu ta kama shi da laifin saɓa wa dokar kwantiraginsa, don haka ta sallame shi daga aiki ɗungurungun.
A yanzu dai Coote yana da damar ɗaukaka ƙara kan hukuncin ladabtarwar da PGMOL ta masa.
Hukumomi uku na bincike
Baya ga PGMOL, ita ma Hukumar ƙwallon ƙafa ta Turai, UEFA ta ƙaddamar da bincike kan alƙalin bayan fitowar wani bidiyo daban da aka ce ya nuna Coote yana shan hodar ibilis, wanda aka ce an ɗauka ne lokacin gasar Euro 2024 a Jamus.
Bidiyon ya nuna wani da ke kamanni da David Coote yana zuƙar 'farin gari' ta hanci, ta amfani da takardar dalar Amurka da aka nannaɗe.
Ita ma hukumar FA mai kula da ƙwallo a Ingila, tana nata binciken kan zargin da Coote ya musanta, na cewa ya taɓa tattauna a intanet tare da wani cewa zai bai wa ɗan wasan Leeds yalon kati gabanin wasa.
Jaridar The Sun ta ce bayan Coote ya ba wa ɗan wasan katin gargaɗn, ya aika saƙo ga wanda suka yi maganar da ke nuna masa cewa ya cika masa alƙawarin da ya ɗauka.
Da ma dai masu sharhi kan wasanni sun yi ahsashen cewa zai yi wuya Coote ya kuɓuta da aikinsa, duba da munin zarge-zargen da ke kansa.