Paul Pogba, dan kwallon Juventus dan asalin Faransa ne. / Hoto : Reuters

Tauraron dan kwallon Faransa, Paul Pogba ya samu hukuncin haramcin buga kwallo na tsawon shekaru hudu daga kotun yaki da shan kwayoyin kara kuzari ta hukumar kwallon Italiya, bayan da aka same shi da laifin shan kwaya a Agustan bara.

Kulob din da Pogba ke buga wa wasa a yanzu, Juventus ya sanar ranar Alhamis, inda kakakin kulob din ya gaya wa AFP cewa an sanar da su game da hukuncin kan dan wasan mai shekara 30, wanda tun a Satumba aka dakatar da shi na wucin-gadi.

Kakakin kulob din ya ce, "Mun samu sanarwa daga kotun a wannan safiya". Sai dai hukumar yaki da shan kwayoyin kara kuzari ta Italiya ba ta amsa neman bayani da AFP ta mata ba.

Masu shigar da kara na hukumar hana shan kwayoyin kuzarin ta nemi a kakaba wa Pogba haramcin shekaru hudu, bayan gwaji ya nuna ya sha kwayar kara kuzari a wasan Juventus da Udenis, inda ya zo a benci kuma ba a saka shi a wasan ba.

Abincin kara kuzari

Wata daya bayan nan, gwajin samfurin B ya kara tabbatar da samuwar sinadarin testosterone a jinin Pogba, inda tun daga nan aka dakatar da shi na wucin-gadi.

Wakilan Pogba sun ce sinadarin testosterone da aka gani ya same shi ne daga abinci mai kara kuzari da wani likita a Amurka ya ba shi shawarar ya ringa ci.

Paul Pogba ya dawo buga wasa a Juventus a karo na biyu a 2022, bayan kwashe shekaru shida a Manchester United, kuma yana cikin 'yan wasan Faransa da suka ci Kofin Duniya a Rasha a 2018, inda ya ci kwallo a wasan karshe da suka buga da Croatia.

An sami Pogba da shan kwayoyin kuzari a lokacin da yake kokarin neman sa'a bayan kakar farko mai wahala a Juventus, inda ya buga wasa sau 10 kacal. Kuma ya samu wasu matsaloli da suka hada da binciken damfara da aka yi kokarin yi masa.

TRT Afrika