Shahararren kulob din kwallon kafa na Masar, Al Ahly ya sha kaye a hannun kulob din Brazil na Fluminense, da ci 2-0 a gasar FIFA ta Kofin Duniya na Kulob-kulob na 2023.
An fitar da Al Ahly, wanda shi ke wakiltar nahiyar Afirka a Gasar Kofin Duniya ta Kulob-kulob ta 2023. Kulob din Fluminense ya doke Al Ahly a wasan dab da na ƙarshe a gasar da kasar Saudiyya ke karɓar baƙunci.
An gwabza wasan ne a daren Litinin a filin wasa na King Abdullah Sports City, da ke birnin Riyadh na Saudiyya.
An hukunta babban dan wasan Al Ahly, Percy Tau bayan da ya kayar da mai tsaron baya na Fluminense, Marcelo Vieira a da'iyar 18, wanda ya janyo aka bai wa Fluminense bugun ɗurme kuma ɗan wasa Jhon Arias ya ci a minti na 71.
Daga bisani John Kennedy ya ƙara wa Fluminense ƙwallo ta biyu a mintunan ƙarshe na wasan.
Al Ahly ta samu damarmakin cin kwallo ta hannun Percy Tau da Mahmoud Kahraba, amma ƙoƙarin nasu bai cimma ruwa ba, sakamakon ƙwararan masu tsaron gida na Fluminense.
Fluminense, su ne zakarun shekarar 2023 a gasar Copa Libertadores ta nahiyar Kudancin Amurka, kuma a yanzu wasa daya ne ya rage musu kafin cin kofin duniya na kulob-kulob, wanda za a buga wasan karshe rana Juma'a.
Kungiyar Ingila ta Manchester City, wadanda ke rike da kofin a halin yanzu, za su kara da kungiyar Urawa Reds ta kasar Japan a Talatan nan, a daya bangaren na wasan dab da na karshe.
Haka nan kuma, za a buga wasan neman matsayi na uku a gasar, wanda aka shirya yi a rana daya da za a buga wasan na karshe.