Ranar Lahadi ne dai Alhassan Yusuf ya fara buga wa Nijeriya wasa mai muhimmanci : Hoto/GettyImages

Kocin tawagar Nijeriya ta Super Eagles, Jose Poseiro ya tabbatar da cewar dan wasan tsakiya na kunfgiyar, Alhassan Yusuf ba zai buga wasan Nijeriya da Ivory Coast ba a Gasar Cin Kofin Afirka (AFCON) da ake yi a Ivory Coast.

Kamfanin dillancin labaran Nijeriya (NAN) ya ambato Poseiro ranar Laraba yana tabbatar da cewa sai a karawar da Nijeriya za ta yi da Guinea Bissau ne dan wasan zai buga wa Nijeriya.

Alhassan Yusuf, wanda ke taka leda a kungiyar kwallon kafa ta Royal Antwerp da ke Belgium, ya ji ciwo ne a wasan farko da Nijeriya ta buga da Equatorial Guinea a gasar AFCON.

An cire Yusuf ne a wasan Nijeriya da Equitorial Guinea bayan ya ji ciwo ranar Lahadi, kuma an tashi wasan 1-1.

Da yake magana da manema labarai a ranar Laraba, kocin na Nijeriya ya tabbatar da cewa Victor Osimhen zai buga wa Super Eagles a karawarsu da Eelephants na Ivory Coast.

TRT Afrika