Ɗan wasan Nijeriya, Alhassan Yusuf ya koma ƙungiyar New England Revolution da ke birnin Boston, na jihar Massachusetts a Amurka.
Alhassan wanda ɗan asalin jihar Kano ne a Nijeriya, a baya yana bugawa Royal Antwerp ta Belgium, inda yake buga wasa a matsayin ɗan tsakiya.
A Belgium, Alhassan ya ci wa Antwerp ƙwallaye shida, da tallafin ƙwallaye 16 cikin wasanni 195 da ya buga tsakanin 2021 zuwa 2024. Ƙungiyar tasa ta ci kofuna huɗu ciki har da kofin gasar Belgian Pro League na 2022–23.
A ranar Litinin ne ya sanya hannu kan kwantiragi da sabon kulob kan kuɗin da aka ce ya kai dala miliyan biyu, zuwa shekarar 2027, tare da zaɓin tsawaitawa zuwa 2028.
Sabuwar ƙungiyar da ake wa laƙabi da The Revs, na buga gasar ƙwallon ƙafar maza ta ajin ƙwararru ta Amurka, wato MLS.
"Muna farin cikin nasarar ɗauko ƙwararren ɗan wasa daga babbar ƙungiyar Turai, Alhassan Yusuf, wanda zuwansa ya ƙara mana ƙarfi a tsakiyar fili," in ji daraktan wasanni, Curt Onalfo a wata sanarwa.
"Alhassan haziƙin ɗan wasa ne da ke da ƙwarewar cin kofi, wanda yake kan ganiyarsa."
A ƙungiyar Super Eagles ta Nijeriya, Alhassan mai shekaru 24, ya buga wa ƙasarsa sau shida. Kuma yana cikin tawagar da ta zo ta biyu a gasar AFCON da aka yi a farkon shekarar nan.