Inter Miami ta lashe Kambun Supporters’ Shield saboda nasarar babban zangon kakar wasa. / Hoto: AFP

Lionel Messi ya ci ƙwallaye uku rigis cikin mintuna 11 a wasan da ƙungiyarsa ta Inter Miami ta lallasa New England Revolution da ci 6-2 a gasar MLS ta Amurka.

Mai shekaru 37, Messi ya ci ƙwallo uku a wasa a karo na biyu cikin mako guda kenan. A wasan na yau, Luis Suarez shi ma ya ci wa Miami ƙwallo biyu tun a zagayen farko na wasan.

Wasan na yau da suka doke New England wadda ɗan wasa ɗan asalin Nijeriya Alhassan Yusuf ke taka leda tun da ya koma can a Agusta, ya bai wa Inter Miami damar samun jimillar maki da ba a taɓa samu ba a babbar gasar MLS ta Amurka.

Miami ta tara maki 74, wato sama da maki 73 da New England ta taɓa kafa tarihin ciyowa a 2021.

Messi ya shigo wasan ne a minti na 58 kuma ya zura ƙwallaye uku a minti na 78, da 81, da 89. A yanzu Messi ya ci jimillar ƙwallaye 20 a wasa 19 na gasar MLS.

Wannan ya bai wa Miami nasarar lashe kyautar Kambun Supporters’ Shield, saboda nasarar babban zangon kakar wasa.

Kofin duniya na ƙungiyoyi

Rahotannun sun ce hukumar ƙwallon ƙafa ta duniya, FIFA ta tabbatar da cewa Inter Miami za ta shiga sahun ƙungiyoyin irinsu Manchester City da Real Madrid, a gasar kofin duniya na ƙungiyoyi wanda aka faɗaɗa.

A cewar shafin ESPN, Inter Miami wanda ke jihar Florida ta Amurka ya samu gurbin wakiltar gasar MLS ta Amurka a gasar da za a yi a bazarar 2025, daga 15 ga Yuni zuwa 13 ga Yuli.

Wannan na zuwa ne bayan da FIFA ta bai wa hukumar ƙwallo ta yankin nahiyar arewacin Amurka, CONCACAF ƙarin gurbi a gasar ta FIFA. Kuma an yi hakan ne saboda a Amurka za a buga gasar, kuma ba hannun MLS a zaɓar Miami.

An faɗaɗa gasar zuwa ƙungiyoyi 32, inda FIFA ta bai wa nahiyar Turai gurabe 12, nahiyar kudancin Amurka 6, sai 4 kowanne ga nahiyoyin arewacin Amurka da Caribbean, da Asiya, da Afirka. Sai kuma sauran gurbin ga nahiyar Oceania.

TRT Afrika