Tsohon dan wasan tsakiya na Chelsea N’Golo Kante ya sayi kulob din kasar Belgium, mai suna Royal Excelsior
Wata sanarwa da aka fitar a ranar Alhamis ta tabbatar da matakin da Flavio Becca ya dauka na sayar da kungiyar ga dan Faransan mai shekara 32, wanda bai dade da komawa kungiyar kwallon kafa ta Al-Ittihad ta Saudiyya ba.
“Flavio ya ji matukar farin cikin mika wa Kante ragamar kungiyar, ba kawai don iya kwallonsa ba har ma saboda dabi'unsa masu kyau," in ji Virton.
Kante ya zama fitaccen dan wasa na baya-bayan nan da ya mallaki kungiyar kwallon kafa.
TRT Afrika da abokan hulda