Hukumar ƙwallon ƙafar ƙasar ta ce Victor Osimhen yana fama da ‘ciwon ciki’. Hoto: Super Eagles/x

Wataƙila shahararren ɗan wasan Nijeriya Victor Osimhen ba zai buga wasan matakin kusa da na ƙarshe ba da ƙasarsa za ta yi da Afirka ta Kudu a birnin Bouake na Ivory Coast ranar Laraba.

Dan wasan gaban Napoli ba ya cikin ’yan wasan da suka yi tafiya a ranar Litinin zuwa birnin Bouake saboda ciwon cikin da yake damunsa, kamar yadda mai magana da yawun tawagar Super Eagles Babafemi Raji ya bayyana.

“Masu kula da lafiyar ’yan wasa sun tabbatar da cewa ɗan wasan yana ƙarƙashin kulawarsu a birnin Abidjan,” in ji shi.

Ya ci gaba da cewa "Idan an sallame shi zuwa gobe (Talata) da safe, zai haɗu da sauran ’yan wasan.”

Gasa mai cike da kalubale

Osimhen wanda shi ne Gwarzon ɗan Ƙwallon Ƙafar Afirka bai yi atisaye ba ranar Litinin gabanin lokacin da tawagar ta kama hanyar barin birnin Abidjan.

An canja Osimhen yayin wasan gab da na kusa da na ƙarshe da Angola ana kusa da tashi wasan a ƙarshen mako.

Dan ƙwallon mai shekara 25 ya ci kwallo daya kuma ya taimaka an ci wata ƙwallon a gasar.

Bayan Nijeriya ta kai matakin wasan kusa da na ƙarshe, Kocin Super Eagles Jose Peseiro ya ce “Ina farin ciki tare da ’yan wasana. Sun cancanci samun wannan nasara.”

“Sun mana komai, ga Super Eagles ga mutum miliyan 220. Sun yi aiki sosai, sun yi aiki sosai, sun yi aiki sosai. Wannan gasa ba ta da sauƙi.”

TRT Afrika