Paulo Fonseca ɗan asalin Portugal ne kuma shekarunsa 51 a duniya. / Hoto: Reuters

AC Milan ta Italiya ta kori kocinta Paulo Fonseca bayan wasansu na ƙarshen makon jiya, inda ƙungiyar ta yi canjaras da Roma da ci 1-1.

A watan Yunin 2024 Fonseca ya karɓi ragamar ƙungiyar inda ya fara jagoranta ta a kakar Serie A ta bana, wadda aka fara a watan Agusta, inda a yanzu bayan watanni shida aka sallame shi.

AC Milan tana mataki na 8 a taburin Serie A, inda take da maki 27 bayan wasanni 17. A wasanninta 5 na ƙarshe, ta yi nasara sau biyu, canjaras sau biyu, da shan kaye sau ɗaya.

A wasansa na ƙarshe Fonseca ya buga kunnen-doki ne da Roma, wadda take mataki na 10 a teburi, inda ya ce ba ya jin ƙamshin zai bar ƙungiyar.

Sai dai yayin da yake barin filin wasa cikin motarsa, ya amsa cewa tabbas sun raba gari da ƙungiyar. Kuma tuni rahotanni ke cewa Milan ta samo wanda zai maye gurbinsa.

Sabon koci

Daga bisani, ƙungiyar ta fitar da sanarwar da ke cewa, "AC Milan tana sanar da cewa ta sallami Paulo Fonseca daga aikinsa na babban kocin babbar ƙungiya ta maza." Sannan ta miƙa godiya ga kocin ɗan asalin Portugal.

Bayan zuwansa Milan a bazarar da ta gabata, Fonseca ya yi rawar gani a wasanninsu na Gasar Zakarun Turai, inda ƙungiyar ke mataki na 12 cikin ƙungiyoyi 36.

Shafin Goal.com ya bayyana cewa rahotanni daga Italiya sun ce Milan za ta naɗa tsohon ɗan wasanta, kuma tsohon kocin Porto, Sergio Conceicao a matsayin sabon koci.

A yanzu za a saurari ganin wane sabon koci ne zai jagoranci AC Milan a wasansu na gaba na gasar Supercoppa, wadda za su kara da Juventus a wasan dab da na ƙarshe ranar 3 ga Janairun sabuwar shekara.

TRT Afrika