Newcastle ta ci wasa daya kacal cikin wasanni 6 da ta buga a baya-bayan nan a gasar Firimiya. / Photo: AP

A tsakar ranar yau ne kolub din Newcastle ya kwashi kashinsa a hannu, a wajen kungiyar Nottingham Forest a gasar Firimiya ta Ingila, inda aka tashi wasa 3 da 1.

Tun a minti 23 ne dan kwallon Newcastle, Alexander Isak ya samu bugun durme, kuma ya ci wa kulob din da ke mataki na 7 a gasar ta Firimiya, kwallon farko. Sai dai a mintin karshe kafin rabin lokaci sai Nottingham ta rama kwallon aka tafi hutu a 1-1.

Chris Wood na Nottingham, wanda tsohon dan wasan Newcastle ne a baya, shi ya farke kwallon, sannan ya karu zura kwallaye biyu bayan an dawo daga hutu, inda ya kammala cin kwallaye uku rigis, a wasan da aka buga a gidan Newcastle din.

A Talatar da ta gabata ne aka cire Newcastle daga gasar Kofin Kalubale na Ingila, wato EFL-Carabao, bayan da Chelsea ta doke ta a bugun daga kai sai mai tsaron gida, bayan an kare wasan canjrasa da ci daya da daya, wanda ya tilasta bugun fenaretin.

Haka nan kuma, mako biyu da suka gabata, an yi waje da Newcastle a gasar Zakarun Turai ta UEFA, bayan da ta kare a mataki na karshe a guruf din F, da maki biyar kacal daga wasanni shida.

Bayan cin wasa daya kacal cikin wasanninsu 6 na baya-bayan nan, alamu suna nuna cewa zai yi wuya Newcastle ta tabuka abin a zo a gani a gasar Firimiyar bana, wanda ita ce gasar da ta rage musu, baya ga gasar kofin FA.

A wasanni hudu da ke gaban Newcastle, za ta kara da manyan kungiyoyi uku, wato Liverpool, da Manchester City, da kuma Aston Villa. Inda a gasar FA za su kece raini da Sunderland ranar 6 ga watan Janairu.

Wannan koma bayan da Newcastle ta samu a watan na Disamba, da kuma kalubalen da ke gabanta na fuskantan wasanni masu tsauri, ya sanya ana kallon babban hadari ne ke fuskantar kulob din da kuma manajansu Eddie Howe.

TRT Afrika